Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan Albarkatun Man Fetur na Nijeriya, Heineken Lokpobiri, ya ce matsakaicin farashin man fetur a Nijeriya har yanzu ya fi na Amurka da wasu ƙasashen Afirka rahusa, duk da cire tallafin man fetur.
Lokpobiri ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today ranar Talata, inda yake kare tsarin cire kayyade farashin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi, a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan tsadar man fetur a sassan ƙasar.
Jawabin ministan ya zo ne bayan da matatun man fetur, ciki har da matatar Dangote, suka rage farashin da suke sayar da man fetur ga dillalai, sakamakon raguwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya. Matatar Dangote ta rage farashin daga N1,350 zuwa N1,325 kan kowace lita, yayin da farashin man a wasu wurare ya ci gaba da kasancewa tsakanin N1,370 zuwa N1,450 kan kowace lita.
Lokpobiri ya ce matsakaicin farashin litar man fetur a Nijeriya ya kai kusan N1,430, yayin da a Amurka yake kusan N1,633. Ya ce a Kamaru farashin ya kai N1,959, yayin da Ghana da Afirka ta Kudu kowannensu ke kusan N2,070 kan kowace lita, bisa bayanan da ya ambata.
Ministan ya kuma ce kasancewar ƙasa na samar da ɗanyen mai ko kuma samun babbar matatar mai ba ya nufin cewa farashin man fetur zai kasance mafi rahusa. Ya yi amfani da Amurka a matsayin misali, yana mai cewa duk da kasancewarta ƙasar da ke kan gaba wajen samar da mai da iskar gas tare da babbar damar tace mai, farashin man fetur a can ya fi na Nijeriya, a cewarsa.
Lokpobiri ya ce farashin man fetur yana dogara ne da wasu abubuwa da dama na kasuwa, don haka kasancewar Matatar Dangote ba ita kaɗai ce ke iya tantance farashin da masu amfani za su saya a gidajen mai ba.
Ya ce tsarin cire ƙayyade farashin man fetur ya samar da damar ƙarin saka hannun jari daga kamfanoni masu zaman kansu a sassan masana’antar mai da iskar gas. A cewarsa, da gwamnati ta ci gaba da shigo da man fetur tare da sayar da shi ƙasa da farashin kasuwa, da hakan ya iya kawo cikas ga gudanar da harkokin matatar Dangote.
Ministan ya ce manufar cire kayyade farashin ita ce bai wa kamfanoni masu zaman kansu damar yin gogayya da juna da bunƙasa harkokinsu a sassan masana’antar mai, ba tare da katsalandan daga farashin da gwamnati ke kayyadawa ba.
A halin yanzu, farashin man fetur na ci gaba da sauyawa a sassa daban-daban na Nijeriya, yayin da ’yan kasuwa ke daidaita farashin man da suke sayarwa bisa sauyin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya, canjin kuɗin waje da sauran yanayin kasuwa.
Raguwar farashin da Matatar Dangote da wasu dillalan man fetur suka yi ta kuma haifar da fatan cewa farashin zai iya ci gaba da raguwa idan raguwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ta ɗore.
