APC ta lashe zaɓen cike gurbin majalisar Kano a Dawakin Kudu

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Dan takarar jam’iyyar APC, Hussaini Yusuf-Datti, ya lashe zaɓen cike gurbin kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar Dawakin Kudu/Warawa, wanda aka gudanar a ranar Asabar.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana Yusuf-Datti a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan kammala tattara sakamakon ƙuri’un da aka kada a mazabun da ke ƙarƙashin mazaɓar.

Yusuf-Datti ya samu ƙuri’a 22,890, inda ya doke ɗan takarar PRP, Habib Hamisu, wanda ya samu ƙuri’a 270. ɗan takarar PDP, Abdullahi Adamu, ya samu ƙuri’a 108, yayin da ɗan takarar APP, Bala Mohammed-Sani, ya samu 53, sannan ɗan takarar LP, Abubakar Yahya-Mohammed, ya samu 39.

Da yake magana jim kaɗan bayan sanar da sakamakon, shugaban APC na ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, Hon. Tijjani Abdulkadir Fedeco, ya bayyana farin cikinsa kan nasarar da jam’iyyar ta samu, yana mai cewa nasarar ta ƙara nuna irin goyon bayan da ’yan jam’iyyar ke samu a yankin.

Fedeco ya ce suna da yaƙinin cewa sabon ɗan majalisar ba zai ba su kunya ba, saboda sun yi la’akari da nagartarsa da kuma sanin yakamata kafin su tsayar da shi a matsayin ɗan takara.

Ya taya Yusuf-Datti murnar lashe zaɓen, tare da bayyana fatan cewa sabon ɗan majalisar zai yi amfani da damar da ya samu wajen tallafa wa ayyukan raya ƙasa da kuma bunƙasa tattalin arzikin yankin.

Haka kuma, ya yi kira ga sauran ’yan takarar da ba su samu nasara ba da su karɓi sakamakon zaɓen, su ci gaba da siyasa cikin lumana, tare da marawa sabon ɗan majalisar baya wajen ciyar da yankin gaba.

Da suke tofa albarkacin bakinsu, wasu daga cikin jagororin APC a Dawakin Kudu, ciki har da Sakataren Ilimi, Hon. Sani Musa Yankatsari, da tsohon Kantomar riƙo na ƙaramar hukumar, Hon. Rabiu Dogo Tamburawa, sun bayyana nasarar da jam’iyyar ta samu a matsayin abin farin ciki ga ’yan jam’iyyar.

Sun yaba wa shugabanni da jagororin jam’iyyar a yankin bisa ƙoƙarinsu na bunƙasa jam’iyyar da kuma tallafa wa ’yan siyasa da sauran al’umma.

Haka kuma, sun yaba wa hukumomin tsaro da jami’an zaɓe bisa yadda aka gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da kuma samar da tsaro har zuwa lokacin sanar da sakamakon.

An gudanar da zaɓen ne domin cike gurbin kujerar Dawakin Kudu a Majalisar Dokokin Jihar Kano, wadda ta samu sarari bayan tsohon ɗan majalisar, Shuaibu Rabiu Nagoggo, wanda aka fi sani da Abba Gano, ya koma Majalisar Wakilai bayan lashe zaɓen cike gurbin kujerar Dawakin Kudu/Warawa ta tarayya.

Jam’iyyun da suka fafata a zaɓen sun haɗa da APC, PRP, PDP, APP da LP, yayin da wasu jam’iyyu suka kasance ba su shiga takarar ba.

By ukarofi

Leave a Reply