Ƙungiyar New England ta Amurka ta ɗauki ɗan wasan Nijeriya Yusuf Alhassan

Spread the love

Ɗan wasan tsakiya na tawagar ƙwallo ƙafa ta Nijeriya, Yusuf Alhassan, ya koma ƙungiyar New England Revolution ta Amurka da taka leda.

Ɗan wasan mai shekara 24 ya koma gasar Major League Soccer ta Amurka ne daga Royal Antwerp ta Belgium, inda ya shafe shekara uku a matsayin ɗan wasan tsakiyarta.

Haifaffen jihar Kano, Yusuf ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara uku da rabi zuwa 2027 tare da zaɓin tsawaita ta da shekara ɗaya.

“Saboda ƙwarewarsa a wasannin ƙasa da ƙasa da kuma gasar zakarun Turai ta Champions League, ina sa ran Yusuf zai nuna kansa a matsayin babban ɗan wasan tsakiya a gasar MLS cikin sauri,” a cewar kocin ƙungiyar Caleb Porter.

A shekarar 2024 Yusuf ya fara buga wa Nijeriya wasa, inda ya buga mata bakwai da suka haɗa da uku a gasar Kofin ƙasashen Afirka ta 2023, da kuma biyu a wasannin neman shiga Kofin Duniya da Nijeriya ta buga da Afirka ta Kudu da kuma Benin.

By ukarofi