Ministar Al’adu na Nijeriya, Barista Hannatu Musa Musawa ta ce haɗin gwiwa da ƙungiyar Dambe Warriors League (DWL) za ta bunƙasa wasannin gargajiya na Nijeriya da tare da bayyana shi a duniya.
Ministar ta bayyana haka ne a lokacin da shugabannin ƙungiyar Dambe Warriors League suka kai mata ziyarar ban girma a Abuja ranar Alhamis.
A cewar wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga Ministar Al’adu da, Nneka Ikem Anibeze, ya fitar a ranar Juma’a, Musawa ta bayyana farin cikinta ga masu shirya gasar da ke da alhakin bunƙasa wasannin gargajiya na Dambe.
“Ma’aikatar tana farin cikin yin aiki tare da Dambe Warriors League. Ta hanyar haɗin gwiwa a wanan ganni, muna da niyyar shigar da ƙwararrun matasan mu da kuma ƙarfafa su a wannan manufa. Wannan haɗin gwiwar za ta zama ginshiƙi don farfaɗo da kyawawan al’adunmu, samar da damar aiki, haɓaka ƙarfin aiki, da haɓaka tasirin al’adun gargajiya.
Tare da goyon bayan ma’aikatar, DWL ta sami damar yin amfani da hanyar sadarwa mai ƙarfi na masu sha’awar wasanni na gargajiya na Afirk. Haɗin gwiwar zai kuma kawo gasar Dambe a kowace jiha ta Nijeriya, tare da nuna tarihin shekaru dubu na al’adun Nijeriya ga matasa maza da mata a duk faɗin ƙasar.
Za a fara sayar da tikitin SuperFight 03 a Abuja velodrome ranar 26 ga Agusta
