Daga MAHDI M. MUHAMMAD
A ci gaba da ƙoƙarin kawar da masu aikata laifuka a ƙasar, shiyya ta ɗaya ta rundunar sojojin Nijeriya ta ɓullo da layin waya don amsa kiran daga sojoji.
Muƙaddashin Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar soji ta daya Laftanar Kanar Musa Yahaya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
A cewarsa, “Bisa la’akari da ƙalubalen tsaro da ake fama da shi a runduna ta ɗaya ta sojojin Nijeriya da ke da alhakin kula da jihohin Kaduna, Neja, Kano da Jigawa, rundunar ta ɓullo da lambar waya kyauta, 08000020204, domin bayar da rahoton matsalolin da suka shafi tsaro.
“Wannan shi ne don baiwa jama’a damar ba da rahoton abubuwan da suka faru na gaggawa tare da kai koke ga Sashen don mayar da martani cikin gaggawa. Har ila yau, a taimaka wa jama’a wajen aike da bayanan da suka dace kan ayyukan ‘yan ta’adda, masu tayar da kayar baya, masu tayar da kayar baya, da ‘yan bindiga da masu alaƙa da su, da kuma sauran batutuwan da suka shafi tsaro da za su taimaka wa sashen da sauran jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyinsu.”
Laftanar Kanar Yahaya ya ci gaba da cewa: “Ku buga layin kyauta kuma ku bi hanyar mu’amala ta murya don bayar da rahoton gaggawa ko gabatar da ƙorafi. A lura cewa duk kira da saƙonnin da aka karɓa akan layi kyauta ne kuma za a bi da su tare da cikakken sirri, yayin da za a ba da cikakkiyar kariya. “
