Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Ƙungiyar PCRC a Jihar Kebbi ta raba wa iyalan ‘yan sanda da suka rasu a bakin aiki kayan abinci.
Da ta ke jawabi yayin bikin a harabar ofishin hukumar ‘yan sanda da ke garin Argungu, Hajiya Saratu Muhammed Mera ta bayyana cewa wannan nauyi ne da ya rataya a wuyansu na ganin ba su yanke hulɗa da marayu da matan ‘yan sanda da suka rasu suka bari ba. Ya zama wajibi su kula da su ko da ta ɓangaren bayar da shawara ne saboda yanzu haka ƙofar wannan ƙungiyar a ko da yaushe buɗe take don karɓar ƙorafi ko shawara daga iyalan ‘yan sanda da suka rigamu.
Hajiya Rafi’atu Hamani shugabar ƙungiyar ta jihohi goma sha tara na Arewacin ƙasar nan ta ja hankalin matan ‘yan sandan da suka faɗi da su tashi tsaye su dage wajen ƙananan sana’o’i na cikin gida don kariyar mutuncinsu da na ‘ya’yansu a maimakon su rinƙa yawace-yawacen neman taimako gidajen mutane.
Ita kuwa uwargidan kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi Hajiya Bilkisu Bello M Sani ta bayyana cewa wannan shine karo na farko da wannan ƙungiyar ta soma ayyana irin wannan aikin a garin Argungu kuma in Sha Allahu za ta cigaba da yin sa tare da inganta shi kowane shekara, haka-zalika a sannu ba za ta bar kowa a baya daga cikin waɗanda ta shafa ba saboda tana kan kowa, idan ba yanzu ba nan gaba saboda kowane mai rai zai mutu.
A ɗaya ɓangaren kuma lokacin da ƙungiyar ta kai ziyarar ban girma fadar Mai Martaba sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera, ya sha alwashin masarautar ita ma ba za a bar ta a bayan nan gaba idan za ƙaddamar da wani bikin a shirye ta ke da ta zuba na ta jari a cikin wannan aikin.
Alhaji Sama’ila Muhammad Mera ya nemi wannan ƙungiyar da ta sanar da masarautar tun da wuri idan Allah ya kai muna rai wata shekara saboda ita ma masarautar ta bayar da na ta gudummawa a cikin wannan aikin alkhairi.
