Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Kiwon dabbobi Alhaji Idi Maiha ya ce Gwamnatin Tarayya za ta share fili mai faɗin hekta 500 a Benuwai domin bunƙasa kiwo.
Maiha ya bayyana haka ne a ranar Asabar a yayin da ya ziyarci cibiyar binciken kiwo ta Benuwai da ke Raaɓ a ƙaramar Hukumar Gwer ta Gabas.
Ya ce, hekta 2,400 da aka ware wa cibiyar ya wadatar domin kiwo, inda ya ce gwamnatin tarayya za ta fara aikin share hekta 500.
Ya yi takaicin yadda cibiyar ke da sama da hekta 2,400, a halin yanzu amma tana da dabbobi 37 kacal, kuma dukkanin kayayyakin da ke cikinta sun lalace kuma suna buƙatar cikakken gyara.
“Za mu kafa wani ƙaramin kwamiti da zai ba da shawarar hanyoyin inganta wannan wuri.
“Muna da burin kafa kamfanoni guda biyu a nan: ɗaya na kiwo, ɗayan samar da abincin dabbobi.
“Hekta 2,400 ya wadatar, don haka da farko za mu share hekta 500 don samun kiwo kafin damina a bana,” ya tabbatar.
Ministan ya ce, kwamitin zai ba da shawarar kan dukka kayan da suka shafi kiwo.
Ya bayyana cewa cibiyar za ta haɗa kai da jami’ar Joseph Sarwuan Tarka da ke Makurdi domin gudanar da bincike.
Yayin da yake jawabi yayin ziyarar, Darakta-Janar na Ofishin Raya Dabbobin Binuwe, Dokta Aondoakaa Asambe, ya ce hakan ya yi daidai da manufar gwamnatin jihar na samar da ofishin.
Asambe ya ce gwamnatin jihar ta yi imanin cewa wuraren kiwon dabbobi za su magance matsalolin tsaro tare da baiwa manoma damar komawa filayen kakanninsu.
Ya ce, gwamnatin jihar ta ɗauki matakin da ya dace na gina masana’antar kiwon dabbobi masu dogaro da kai wanda zai kawo fa’ida ga tattalin arziki.
Ya yaba wa gwamna Hyacinth Alia bisa goyon bayan ofishin domin samun nasarar aikin bunƙasa kiwo.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ya ruwaito cewa tun da farko Ministan ya ziyarci aikin inganta aladu da amfanin gona na Benuwai, Yadeɓ, ƙaramar hukumar Gboko, da kuma kasuwar shanu ta duniya, Makurdi.
