Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jimillar kuɗaɗen shigar da ake samu a Asusun Tarayya daga harajin ɓAT a watan Fabrairun 2025 ya ragu da Naira biliyan 117.430, daga Naira biliyan 771.886 a watan Janairun 2025 zuwa Naira biliyan 654.456 a watan Fabrairu.
Wannan raguwar, tare da raguwar kuɗaɗen shiga daga harajin Ribar Man Fetur (PPT), Harajin Kuɗi na Kamfanoni (CIT), harajin shigo da kaya, da kuma harajin CET, ya shafi jimillar kuɗaɗen shigar da ake samu na rarraba wa ga matakai uku na gwamnati a watan Fabrairu.
A cikin sanarwar da Kwamitin Raba Kuɗaɗen Asusun Tarayya (FAAC) ya fitar a ƙarshen taron sa na watan Maris 2025 a Abuja, jimillar kuɗaɗen shiga na Naira tiriliyan 1.653 da aka raba a taron na watan Maris ya yi ƙasa da Naira tiriliyan 1.848 da aka samu a watan Janairun 2025 da Naira biliyan 194.664.
FAAC ya bayyana cewa, jimillar kuɗaɗen da ake rabawa na Naira Tiriliyan 1.678 sun haɗa da kuɗaɗen da aka raba bisa ƙa’ida na Naira biliyan 827.633, kuɗaɗen harajin haraji ɓAT na Naira biliyan 609.430, kuɗaɗen da ake rabawa na EMTL na Naira biliyan 35.171, Harkar Ma’adanai na Naira biliyan 218.
Taron na FAAC wanda Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun ya jagoranta, ya kuma samu halartar sabon Akanta Janar na Tarayya, Shamseldeen Ogunjimi.
A cikin sanarwar, an samu jimillar kuɗaɗen shiga na Naira Tiriliyan 2.344 a watan Fabrairun 2025. Jimillar kuɗaɗen da aka cire na kuɗaɗen da aka tara sun kai Naira biliyan 89.092, yayin da kuɗaɗen ajiya suka kai Naira biliyan 577.097.
Ya bayyana cewa, daga jimillar kuɗaɗen shigar da ake rabawa na Naira Tiriliyan 1.678, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira Biliyan 569.656, Gwamnonin Jihohin ƙasar kuma sun karɓi Naira Biliyan 562.195, ƙananan Hukumomi sun samu Naira Biliyan 410.559, da Jimillar Naira Biliyan 136.042 (kasancewar kashi 13 cikin 100 na kuɗaɗen shiga na ma’adinai) an raba su tare da jihohin da ke cin gajiyar arzikin ma’adinai.
Daga nan kuma ya bayyana cewa daga cikin kuɗaɗen shigar da aka samu na Naira biliyan 609.430 na ɓAT, gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 91.415, gwamnatocin Jihohi kuma sun karɓi Naira biliyan 304.715, sannan majalisun ƙananan hukumomi sun samu Naira biliyan 213.301.
Jimillar Naira Biliyan 5.276 ne Gwamnatin Tarayya ta samu daga cikin Naira Biliyan 35.171 na harajin EMTL. Gwamnonin Jihohi sun karɓi Naira Biliyan 17.585, ƙananan Hukumomin kuma sun karɓi Naira Biliyan 12.310.
