Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
An bayyana cewa samar da aikin asibitun kula da lafiyar ƙoda da wanketa kyauta da kawo aikin gina makarantar koyon aikin jinya da unguwar zoma da ɗan Majalisa mai wakiltar ƙaramar Hukumar Sule Tankarkar, Maigatari, Gagarawa da ƙaramar Hukumar Gumel Hon. Nazifi Sani Fulawa ya yi a wannan mazaɓa tashi a bun a yaba ne, kuma akwai buƙatar ‘yan majalisa da sauran shugabanni su yi koyi da wannan wakili wajen kawowa al’ummarsa cigaba a wannan lokaci.
Hajiya Hauwa Gumel, mai bai wa Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi ɗanmoɗi shawara kan wayar da kan mata, a shiyya ta Arewa Maso Yamma ta bayyana haka a lokacin bikin gangamin raba kayan tallafin abincin Azumin Ramadan da wakilin waɗannan ƙananan hukumomi huɗu ya gabatar a masarautar Gumel a ranar Lahadi da ta gabata.
Haka kuma ta ƙara da cewa babu shakka wannan wakili da su ka zaɓa a wannan yanki ya fitar da su kunya domin yanzu ga tallafin abinci irin su, taliya, shikafa, masara da sauransu ya kawo tallafi ga al’ummarsa na waɗannan ƙananan hukumomi huɗu da aka ƙiyasta dubun dubatar al’umma ne a wannan yanki za su amfana wannan, inda ta ce wannan baƙaramin cigaba ba ne kuma koyi ne da gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi ɗanmoɗi kuma hanya ce ta sauke nauyin da aka dora masa bayan zaɓensa da aka yi a karo na biyu a jam’iyya APC, a cewar Hajiya Hauwa Gumel.
Tun da farko Hauwa Gumel, sai da ta yaba wa Gwamnan Jigawa Malam Umar Namadi ɗanmoɗi kan wani babban tarihi da ya kafa a wannan jiha na ciyar da al’umma abincin buɗe-baki wanda yake tare da alheri mai yawa a wannan ciyarwa wanda tace tsarin da aka yi a Jihar Jigawa tsari ne mai kyau wajen ciyarwa da abincin buɗa baki domin an karkasa abin waje-waje ta yadda al’umma za ta amfana wanda a nan ƙaramar hukumar Gumel aƙalla ana ciyar da mutum dubu 30 a kowacce rana kamar yadda abin yake a sauran tsananan hukumomun Jihar Jigawa baki ɗaya daidai gwargwadon yadda al’umma za su amfana a yankinsu kuma abun la’akari shi ne gwamna ya tsara cewa dole komai na abincin a siya a Jihar Jigawa tun da ga kan gero, tsamiya, itace, mai, wake, da sauran duk abun da ake amfani da shi na girki ga kuma alawus da ake bawa mata masu aikin na Naira 3000 kowacce rana, wanda kafin wannan kuma an bawa dubunnan mata jarin Naira 100,000 daga gwamna ɗanmoɗi domin bunƙasa sana’o’insu don ciyar da Jigawa gaba ta kowane fanni.
