Daga DAUDA USMAN a Legas
A ranar Juma’ar da ta gabata ne haɗɗiyar ƙungiyar Masu Kasuwancin Kayan Gwari da Noman ta ƙasa a Nijeriya ƙarƙashin jagorancin shugabanninta na ƙasa ta gudanar da taron ta a Kano.
Taron wanda ya gudana a gidan GRA da ke unguwar Nasarawa cikin garin Kano, ya ƙunshi dukkan masu ruwa da tsaki a bisa kan harkokin kasuwancin gwari da nomanta a Nijeriya bakiɗaya.
Babban magatakardar kasuwar ƙasa da ƙasa da ke birnin Legas a kasuwar mile12 Intanashinal maket, Alhaji Idiris balarabe shi ne ya wakilci babban shugaban kasuwar Alhaji shehu Usman jibirin samfam kuma shugaban ƙungiyar kasuwannin al ummar Hausawa na Jihar Legas gabaɗaya a wajen taron, sannan shi ne ya jagoranci gudanar da taron bakiɗaya.
Iyayen taro sun haɗa shugaban ƙungiyar Dattawan kasuwar Alhaji Isah mohammed mai shinkafa mile12 wanda ya samu wakilcin sakataren ƙungiyar dattawan kasuwar Alhaji Abdulwahab Tsoho Babangida da tsohon shugaban kasuwar Alhaji Haruna Mohammed tamarke da Alhaji Abdullahi Burama da sauran makamantansu.
Mai masaukin baƙi a wajen taron shi ne babban shugaba mai kulawa da kawo cigaban kasuwancin tumatiri a Legas Alhaji Abdulgiyasu Sani Rano mahalarta taron sun haɗa da shugaban ƙungiyar masu safarar dabbobi da kayan abinci ta ƙasa Dakta Alhaji Mohammed Shattima da sauran manyan baƙi.
Kaɗan daga cikin shuwagabannin ɓangarorin kasuwar ta mile12 Intanashinal maket a wajen taron akwai Alhaji Abdullahi Tukur kura shugaban ƙungiyar shuwagabannin ɓangarorin kasuwar ta mile12 da Abdulgiyasu Sani Rano shugaban ɓangaren tumatiri a Legas da Alhaji Aminu Musa Kiru shugaban ɓangaren tattasai da tsohon shugaban ɓangaren tattasai Alhaji Dauda Tarai da shugaban ƙungiyar karas da kabeji Alhaji Bala Yaro Hunƙuyi da tsohon shugaban ƙungiyar karas da kabeji na lardin zazzau Alhaji Ibirahim ɗan Daɗa Hunkiyi da sabon shugaban na lardin zazzau Alhaji Sa’idu malfar kuɓewa hunkuyi da sauran waɗansu shuwagabannin ƙungiyar waɗanda suka fito sassa daban daban na jihohin kasar nan bakiɗaya.
Alhaji mahammadu Abdu, shugaban gudanarwar kasuwar ta mile12 bakiɗaya shi ne ya tsara taron kuma aka gabatar da shi a daidai wannan lokaci a jawabansa na wajen taron babban magatakardar kasuwar ta mile12 Intanashinal maket Alhaji Idiris Balarabe ya tabo muhimman shawarwari waɗanda za su cigaba da bunƙasa harkokin noman gwari da kasuwancin ta a Nijeriya bakiɗaya
Sannan aka ba waɗansu daga cikin mahalarta taron suka gudanar da nasu jawaban tare da gabatar da ƙorafe-ƙorafen su gaba ɗaya.
