Yadda mahauta ke ƙara neman haɗin kan junansu a Legas – Ado Garba

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Wani babban mahauci a Legas mai suna Alhaji Ado Garba ɗan asalin jihar Kano wanda ake mai laƙabi da suna Alhaji Ado Garba Araba aba kowa dake babbar mayankar shanu ta abbatuwa Okoba Agege Legas, ya shawarci mahautan jihar Legas da ma na ƙasa bakiɗaya da su ƙara ƙoƙari a wajen haɗa kawunan junansu tare da bunƙasa harkokin sana’arsu ta fawa a Legas da kewayenta gabaɗaya.

Alhaji Ado Garba Araba Abakowa ya yi wannan tsokaci ne a ofishinsa dake babbar mayankar shanu ta abbatuwa Legas jim kaɗan bayan kammala wani ɗan kwarya-kwaryan taron da suka shirya domin tattaunawa bisa ga matsalolin da sana’ar fawa ke fuskanta a Legas tare da nemo hanyoyin warware matsalolin gabaɗaya.

Taron ya samu halartar waɗansu daga cikin masu ruwa da tsaki bisa kan harkokin sana’ar fawa na mayankar shanu ta abbatuwa dake cikin birnin Legas.

Mahalarta taron sun gabatar da jawabai ɗaya bayan ɗaya. Bayan kammala jawabansu ne Alhaji Ado Garba Araba abakowa ya shawarci Gwamnatin Jihar Legas da ta cigaba da tausaya masu ta fuskar kuɗin harajin kasuwar ta mayankar shanun da suke biya da sauran al’amuran da suka shafi mayankar shanu gaba daya haka zalika ya cigaba da shawar tar mahautan na legas dasu Kara kokari a wajan tsaftace sana’ar su tafawa a Legas tare da yi wa jama’a hannu yasan na gida a lokacin da suke gudanar da harkokin sana’arsu ta fawa a Legas.

Haha kuma ya cigaba da shawartar mahautan da su ƙara ƙoƙari a wajen kawo abubuwan da za su cigaba da wanzar da zaman lafiya a tsakanin mahautan Hausawa da na sauran ƙabilu mazauna jihar Legas gabaɗaya.

Bugu da ƙari ya cigaba da cewa zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki saboda haka ya ce ya zama wajibi ƙabilun mahautan guda biyu su cigaba da zaman lafiya a tsakaninsu.

Ya kuma yi fatan Allah Ubangiji ya cigaba da zaunar da jihar Legas lafiya da sauran jihohin dake cikin Nijeriya baki ɗaya.

By ukarofi