Ƙungiyar ’yan kasuwa ta Abuja za ta zuba jari a Amurka

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar ’yan kasuwa da masana’antu ta Abuja (ACCI), ta buƙaci ’yan kasuwar Nijeriya da su yi amfani da jerin bayanan zuba jari da za su yi don mallakar kasuwanci a Amurka.

Shugabar ƙungiyar na ACCI, Victoria Akai, ta yi wannan bayani a ranar Laraba a wani taron manema labarai a Abuja, don bayyana jerin bayanai kan damar zuba jari a Amurka, mai taken; ‘EB-5 Fasfo Series’.

Taron wanda aka shirya gudanarwa a ranar 20 ga watan Oktoba a cibiyar hada-hadar kasuwanci ta ACCI da ke Abuja, kamfanin ‘Invest In the USA’, IIUSA, tare da haɗin gwiwar ACCI ne suka shirya shi.

A cewar Akai, EB-5 Passport Series, hanya ce ta mallakar kasuwanci a Amurka tare da zama na dindindin.

“Yawancin masu saka hannun jari a Nijeriya a Amurka, muna da damar da za mu ba da gudummawa don tsara manufofin da suka shafi Nijeriya da ’yan Afirka a Amurka.

“A bisa ƙididdigar bankin duniya, Nijeriya a shekarar 2019 tana da jimillar dala biliyan 53.6 da aka shigo da ita dala biliyan 47, wanda hakan ya kai ga samun daidaiton ma’auni na kasuwanci na kusan dala biliyan biyu.

“Ana neman ’yan Nijeriya da su zo su saka hannun jari a Amurka kamar yadda sauran ƙasashe ke zuwa su zuba jari a Nijeriya, su samu kuɗi, su ɗauki ’yan ƙasarsu aiki, kuma duk wata ribar da muka samu a Amurka, mu ma an bar mu mu mayar da ita Nijeriya.

“Daga ƙarshe, a cikin shekara guda ya kamata mu iya dawo da dala biliyan ɗaya ko biliyan biyu zuwa gida Nijeriya,” inji ta.

A cewar Akai, da yawa daga cikin ’yan Nijeriya da ke neman halaltaccen saka hannun jari a Amurka, ba sa cuɗanya da mutanen da suka dace, ko samun ingantattun bayanai da za su ba su damar gudanar da harkar yadda ya kamata da kuma ba da tabbacin samun nasara cikin lokaci.

“A matsayinmu na ƙwararru a fannin ciniki da saka hannun jari na ƙasa da ƙasa, mun fahimci yadda ake amfani da kasancewar ’yan ƙasa na gaskiya a ma’anar motsin duniya.

“Damar saka hannun jari, wanda kuma ke ba da dama ga zama ɗan qasa, na iya taimakawa wajen faɗaɗa tasirin tattalin arzikin mutane da kuma taimaka musu su gina fiye da iyakoki da kasuwanci da rayuwa ba tare da iyaka ba.

“Tsarin saka hannun jari a Amurka shine yuwuwar havaka mai da kuɗaɗen zuwa Nijeriya.

“Masu zuba jari na Nijeriya za su iya cin gajiyar yarjejeniyoyin nahiya da na kasuwanci daban-daban da ake da su a Amurka kamar yarjejeniyar ciniki cikin ’yanci ta Arewacin Amurka (NAFTA),” inji Akai.

By Editor