KKDA ta bai wa mata 95 jari a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Ƙungiyar ci gaban unguwar Kumbiya-kumbiya Development Association (KKDA), ta gina azuzuwan karatu da kuma manyan kwalbatoci uku a unguwar, sannan ta sama wa wasu mata 95 jarin naira dubu 10 don bunƙasa sana’oinsu.

Shugaban ƙungiyar, Dakta Ahmed Yarmama shi ne ya bayyana hakan, inda ya ce, a Gombe ƙungiyar ta zama abin misali da wasu unguwanni suke zuwa kwaikwayon irin ayyukan da suke yi.

Ya ƙara da cewa, sun tara kuɗin ƙungiyar ne a banki, inda daga baya ya ga ci gaba da ajiye su bai da amfani gara su gyara unguwarsu kuma su taimaki ‘ya’yan unguwar, wanda hakan ya sa suka zaƙulo mata masu ƙananan sana’oi guda 95 suka basu jarin naira dubu goma-goma bashi da za su biya cikin sati goma.

Dakta Ahmed Yerma ya ce, “ganin talauci ya yi yawa ne kuma matan a wasu lokuta suna taimakawa mazajensu da suka ‘ya’yan shi ya sa ya ga da cewar ɓullo da wannan tsari idan ya ga sun dawo da shi sai a bai wa wasu ma su kuma a ƙara musu ya kai dubu 30 wanda idan suka ga mace ta tsaya da ƙafarta sai su bar mata jarin ya zama an taimake ta.”

Ya ƙara da cewa, “dalilinsu na taimakawa matan shi ne wata jarin ta bai wuce naira dubu biyar amma yanzu an basu dubu goma ai an taimake su”.

Har ila yau ya qara da cewa, bayan matan za a duba matasa suma a inganta musu nasu sana’oin irin masu aski da sayar da katin waya da sauran irinsu.

Daga nan sai ya ce, sun samar wa yara da yawa ayyukan yi wasu kuma an sama musu makarantun gaba da sakandare da nufin za a taimakawa karantun nasu muddin iyayensu ya zama basu da ƙarfi ci gaba da ɗaukar nauyin karatun nasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *