Gidauniya Hausari za ta sa ’ya’ya mata 150 makaranta kyauta a Yobe

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wata gidauniya mai rajin haɓaka harkar ilimin ’ya’ya mata a jihar Yobe, ‘Hausari Female Education Support Foundation’, za ta saka yara mata 150 makarantun boko kyauta a jihar.

Shugabar gidauniyar, Hajiya Hafsatu Alhaji Ado, ta ce, za su ba da tallafin ne a ƙoƙarinsu na mara wa aniyar gwamnatin jihar baya wajen inganta ilimim ’ya’ya mata.

Ta bayyana hakan ne a lokacin da ta ke zantawa da manema labarai a Gombe ranar Lahadi, inda ta ce, ciyar da ilimin ’ya’ya mata gaba ne maƙasudin kafa gidauniyar tasu.

Hajiya Hafsatu ta ce, gidauniyar sabuwa ce da aka ƙirƙire ta da manufar yin koyi da kyawawan manufofin gwamnan jihar, Yobe Mai Mala Buni, wajen rage yawan mata da ba sa zuwa makaranta a jihar.

A cewarta, za ta cimma wannnan buri ne ta hanyar shigar da yara matan makaranta da kuma ta ɗaukar nauyin mayar da waɗanda suka daina zuwa makarantar.

Daga nan Hafsatu Ado ta ƙara da cewa, bayan mayar da mata 150 sun koma makaranta, za ta sake mayar da wasu 20 ɗin da suka daina zuwa makaranta tare da ɗaukar cikakken nauyinsu.

By Editor