Daga CMG HAUSA
A yau Litinin aka ƙaddamar da gasar tsara bidiyo ta matasan Sin da Afrika mai taken “Great to Meet You” ta babban gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin wato CMG, wanda ke zaman wani yunƙuri na ganin kyan bangarorin biyu da kuma ƙulla abota.
Manufar wannan gasa ita ce, amfani da gajeren bidiyon da aka tsara wajen samar da dandalin musaya da koyo daga juna tsakanin matasan Sin da Afrika, da bayyana salon matasan Sin da Afrika tare da inganta ɗorewar abota tsakanin Sin da Afrika.
Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa
