Ƙungiyoyin aikin gayya 160 ne gwamnatin Kano ta raba wa kayan aiki – Hon. Durbundai

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

An bayyana ce wa ƙungiyoyin aikin gayya 160 ƙarƙashin shugabancin shugaban ƙungiyar aikin gayya na kwamitin ƙoli na Jihar Kano Alhaji Ibrahim Garba Aminu Ƙofar Na’isa, Gwamna Abba ya yi bikin raba musu kayan aiki yashe kwata da share kwalbatoci a ƙananan hukumomi birni takwas domin kawar da barazanar ambaliyar ruwa da ke fuskantar waɗanan ƙananan hukumomi kamar yadda hukumar NEMA ta yi hasashe a wannan damina, kamar dai yadda mai ba gwamnan Kano shawara akan harkokin ƙananan hukumomin Kano Hon Garba Umar Durbunde, tsohon ɗan majalisar jiha da tarayya kuma tsohon kwamishinan raya karkara kuma shugaban kwamitin yashe magudanan ruwa na Kano ya bayyana haka a wajen taron ƙaddamar da raba kayayyakin aikin yashe magudanan ruwa da aka raba wa ƙungiyoyin 160 a ranar Litinin ɗin nan da ta gabata.

Haka kuma ya ƙara da cewa kayayyakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya raba wa waɗanan ƙungiyoyi 160 masa bada gudumawa don tsaftace Kano sun haɗa da wulbaro kimanin 600 sai takalma, safar hannu, diga, manjagara, suma ɗari shida shida, sai akwatinan magani na matakin farko a kiwon lafiya da ake kira First Aid da dai sauransu domun amfanin waɗanan ƙungiyoyi aikin gayya na sa kai da zasuyi wannan aikin dan tsafta ce dan yashe kwatoci da kwalbatocin Kano.

Hon Durbunde, ya bayana cewa a matsayinsa na wanda gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya naɗa a matsayin shugaban wannan kwamiti na yashe kwatocin ƙananan hukumomun cikin birnin Kano takwas a kawai kwamishi nan raya karkara Hon Abbas Sani Abbas, sai kuma kwamishi nan kula da mahali Hon Nasiru Sule Garo, da sauran mambobi wanda sunkai su 13 yan kwamitin wannan aikin kuma zasuyi kwana 14 ne suna wannan aiki domun kawai da wannan barazana ta ambaliyar ruwa a wannan yanki kuma abun za a faɗaɗa shi zuwa sauran ƙananan hukumomi 36 bayan waɗanan takwas na cikin burni.

Haka zalika kuma za a yi amfani da manyan motocin aiki domin haƙa ramukan ko kwalbatoci da suka cike a wannan lokaci kuma abin ya haɗa har da ƙungiyoyi na Majalisar Ɗinkin Duniya masu rajin kare muhalli domin dai kawar da wannan barazana wanda ya ce wannan ƙoƙari na gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya nuna cewa kano na zuciyar Abba, domun samar da yanayi mai kyau ga al’ummar kano a ko wanne fanni.

Ita ma sakatariya a ma’aikatar raya karkara Hajiya PS Binta Lawan Aliyu, ta ce abun farinciki ne yadda gwamna ya taimakawa waɗanan mutane masu sadaukar da kai da yin aiki tuƙuru domin Allah da kishin al’ummarsu jiharsu da ƙasarsu.            

Shi ma a jawabinsa shugaban ƙungiyar kwamitun aikin gayya na ƙoli Alhaji Ibrahim Garba Aminu Ƙofar Na’isa, ya ce a shekaru 8 da suka wuce basu samu wannan dama ba amma gashi yanzu gwamnan Kano ya talafa musu da kayan aiki mai yawa sosai.

By ukarofi