
Daga BELLO A. BABAJI
Sadiq Abacha, wanda ɗa ne ga marigayi tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, ya ƙudiri aniyar bai wa mahaifinsa kariya, inda ya ce shugabancin da ya yi a Nijeriya abin alfahari ne ga al’umma.
A wani rubutu da aka wallafa a shafin Facebook, ya ce Abacha ya fuskanci ƙalubale na ƙyashi da butulci, amma duk da haka tarihi ba zai manta da gagarumar hidimar da ya yi wa ƙasa.
Ya ce, duka irin ƙyashin da ake yi wa mahaifin nasa, har yanzu yana alfahari da shi a matsayinsa na wanda wasu a yau suka so ace dama sun kwaikwayi ko da rabi ne daga halayensa.
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan fitar da littafin ‘A journey in Service’ na Tsohon Shugaban mulki soji, Ibrahim Badamasi Babangida, IBB, wanda hakan ya haifar da tattauna batutuwa da dama.
Babban batun da al’umma suka fi mayar da hankulansu a kai shi ne shelanta MKO Abiola a matsayin halasttaccen wanda ya lashe zaɓen 12 ga Yuni na 1993, wato ‘June 12’ da IBB ya yi, wanda aka murɗe.
Tsohon Shugaban ƙasar ya bayyana cewa ya yi da-na-sanin hukuncin, wanda ya zargi wasu sojoji daga cikin ƴan gwamnatinsa ƙarƙarshin jagorancin Abacha suka shirya ba tare da sanar da IBB ba.
Marigayi Sani Abacha dai shi ne wanda ya mulki Nijeriya daga 1993 har zuwa lokacin rasuwarsa a 1998, kuma ɗaya ne daga cikin shugabannin da aka fi tafka muhawara akansu.
