
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar zaɓe ta Jihar Osun (OSSIEC), ta sanar da Jami’iyyar PDP a matsayin wadda ta lashe duka kujerun ciyamomin jihar a zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar.
Shugaban Hukumar, Hashim Abioye ya bayyana hakan ta kafar Facebook a daren ranar.
Ya kuma ce, ƴan takarar kujerun kansiloli na jami’yyar suma sun lashe zaɓe a duka gundumomin 332 dake jihar, kamar yadda PDP’n ta lashe na ƙananan hukumomi 30 dake faɗin jihar.
Da farko dai shugaban na OSSIEC ya zargi jami’an tsaro da rufe babban ofishin hukumar don hana isar da wasu daga cikin kayayyakin gudanar da zaɓen zuwa ga mazaɓunsu.
Ga jaddawalin zaɓaɓun ciyamomin da ƙananan hukumominsu kamar yadda Blueprint ta ruwaito:
Babalola Wasiu Kayode – Boripe
Okunade Oluwafemi Adesanya – Egbedore
Adeyenuwo Rotimi John – Ife Central
Agboola Francis Olajire – Obokun
Azeez Lateef Adeniran – Isokan
Aina Abayomi Adesina – Boluwaduro
Sodiq Samuel Oluwapelumi – Ola Oluwa
Ajibade Oluwatoyin S. – Irepodun
Adebanjo Oladiti Tunmininu – Ilesa West
Ibironke Alade Adegboye – Atakumosa East
Aroke Muyiwa Aderemi – Ife South
Kolade Obafemi Kolawole – Olorunda
Moshood Adekunle Kabiru – Iwo
Awotunde Abiodun Sarafadeen – Ifelodun
Akande Taiwo Adekunle – Osogbo
Dada Feyisayo Ajibola – Atakumosa West
Amodu Taiwo – Ede North
Atolagbe Kayode Olayinka – Ifedayo
Akande Michael O. – Ife North
Adeyekun Taiwo Adebayo – Oriade
Adeniran Adenike Felicia – Ayedaade
Afolabi Oyekola Lukman – Ede South
Odunyemi Haruna Bukola – Ife East
Jooda Ambali Babajide – Irewole
Adewale Adeyinka Oluwaseun – Odo Otin
Ogunbiyi Solomon Akinyemi – Ayedire
Raimi Adenike Nafisat – Ejigbo
Adebisi Jayeola Nasir – Ila
Ilesanmi Taiwo Sunday – Ilesa East
Alade Aderemi Fatai – Orolu
