A tausayawa mata da masu ƙaramin jari

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A ƙarshen makon da ya gabata, an yi wani abu da ya faranta min rai kuma ya canza min tunani game da yadda masu hali da ’yan siyasa ke taimakawa jama’a masu rauni da mabuƙata a cikin al’umma. Kodayake, ba duka aka taru aka zamo ɗaya ba, kuma akasari abubuwan da gwamnati ko ’yan siyasa ke yi na tallafawa jama’a suna yi ne domin jama’a su gani a faɗa, saboda gyara siyasar su. Amma ko da akwai hakan, in dai jama’a za su amfana, su ci moriyar dimukraɗiyya, aaallah za a ce sambarka!

Abin da ya faru kuwa shi ne, wani matashin ɗan siyasa ne da ba a jima da zaɓarsa ba, a matsayin Kansila a wata unguwa da ke ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, ya yi wani abin a zo a gani, da ya birge jama’a, bisa irin ayyukan tallafawa raunana cikin talakawa, da ya aiwatar a ɗan ƙanƙanin lokacin da ya yi a kujerar wakilcin unguwar Abba Na Shehu da ke cikin garin Jos.

Ba kamar yadda akasarin ’yan siyasa suke yi ba, idan za su yi rabon kayan abinci ko tallafi, sai sun tara mutane a harabar gidajensu, an gayyato ’yan jaridu da masu ɗaukar hoto, don duniya ta gani, ba saboda tausayi ko kishin al’umma ba. Ko da kuwa wasu ’yan siyasar sun so yi a ɓoye, na kusa da su ba za su bari ba.

Shi wannan matashin ɗan siyasa da na ambata muku a baya, Honarabul Auwal Hassan Tubarkallah, ya yi abin da ya birgeni sosai. Duk da kasancewar har yanzu Jihar Filato ba ta fara amfani da dokar bai wa wakilan al’umma na ɓangaren ƙananan Hukumomi damar cin gashin kansu ba, amma shi a matsayinsa na Kansila ya rarumo wasu kuɗaɗe da ya gudanar da wasu ayyuka na taimakawa talakawa da masu tsananin buƙatar taimako, don gudanar da sana’o’in dogaro da kai da za su rufa wa kansu asiri da iyalinsu.

Daga ciki akwai waɗanda suka amfana da tallafin kuɗaɗe na yin jari don su samu sana’ar yi, akwai waɗanda suka samu kyautar buhun gawayi da za su riƙa sayarwa, akwai waɗanda aka bai wa jarin rake don sayarwa, akwai kuma masu sana’ar sayar da kayan lambu, da masu sayar da ruwan wanka da safe, su ma an ba su garwar dafa ruwan har da itacen hura wuta. Sannan akwai masu sana’ar haɗa takalma na sayarwa, da matasa masu sayar da man fetur a jarkoki da a wasu wuraren ake ce wa, ’yan bunburutu. Da masu aikin haƙar kuza da aka saya musu diga da cebur, don aikin tono ma’adanin kuza da gyara ta.

A taƙaice dai, kayan sun haɗa buhun gawayi 10, jarkokin fetur masu cin lita 25 guda 5. Da kuma kayan lambu da suka haɗa da buhunan kabeji 8, da buhunan karas 8, waɗanda su kuma aka raba wa matasa 16. Sannan akwai garewanin dafa ruwan wanka da itace da aka bai wa mata 3, sai kuma aka raba takalma da aka haɗa a gida dozin 3 ga wasu mata 4, don su samu abin sana’a.

Akwai jarin rake ɗauri 3 da aka bai wa wasu matasa, maza da mata, masu sana’ar dogaro da kai. Yayin da aka raba wa mata 10 masu sana’ar sayar da kayan miya a cikin gidaje, kwandon tumatir 3 da tattasai buhu 3, kwandon kubewa 3, da albasa buhu 3. Bayan jarin Naira dubu goma-goma da Hon. Auwal Tubarkallah, ya raba ga wasu matasa 5 masu ƙananan sana’o’i.

Babu shakka irin wannan taimako da Kansilan Abba Na Shehu ya yi, irinsa ake so ’yan siyasa da sauran masu halin bayar da taimako su riƙa yi a cikin al’umma. A riƙa duba mutanen da suka cancanci samun wannan taimako saboda halin da suke ciki, su da iyalansu, ba tare da nuna sani ko sabo ba. Mai karatu, ina ma a ce kana wajen da aka yi wancan rabon tallafin, da kaso ka ga yadda fuskokin waɗannan bayin Allah suka nuna, saboda jin daɗin abin da aka yi musu, musamman ma a yanzu da ake dab da shiga watan azumi.

Yana da muhimmanci masu hannu da shuni da waɗanda Allah Ya horewa, su duba a cikin maƙwaftansu da ’yan uwansu, har ma da waɗanda suke hulɗa da su yau da gobe, a ga waɗanda suke matakin farko na buƙata, a taimaka musu, ko da kuwa da ɗanyen abinci ne ko dafaffe na buɗe baki. Gwamnati a dukkan matakai ta ɓullo da wani shiri da zai ƙara sauƙaƙa farashin kayan abinci a kasuwanni, kamar yadda rahotanni suka nuna cewa Gwamnatin Jihar Neja tana son yi, saboda talakawa su samu sauƙin rayuwa cikin azumin nan.

Sannan ga jihohin da suka saba ware wani abu na taimako a cikin watan Ramadan da ƙungiyoyin jama’a, su ma su ƙara ruɓanya abin da za su bayar fiye da na baya, don ya isa ga jama’a da dama. Alal-haƙiƙa, jama’a da dama na cikin halin ƙuncin talauci sosai, masu ƙananan kasuwanci jari ya karye, karatu ya gagari yaran talakawa da dama, duk da cewa da ake yi farashin kayan abinci yana sauka, amma rayuwar ’yan Nijeriya ta zahiri ba ta sauya ba har yanzu.

Da fatan za mu shiga cikin azumi cikin nasara, kuma mu mayar da hankali ga ibada da addu’o’i, don samun rufin asiri da zaman lafiya a garuruwanmu da ƙasa bakiɗaya.

By ukarofi