Ba Ned ne uban cikin da nake ɗauke da shi ba – Jaruma Chika Ike

Spread the love

Daga AISHA ASAS

A ‘yan kwanakin nan ne kafafen sada zumunta suka yi amo da labarin ciki da fitacciyar jaruma a masana’antar Nollywood Chika Ike ke ɗauke da shi, wanda aka shiga muhawar wanda ya zama silar samun cikin nata.

kasancewar jarumar ba ta ce kamai ba, ya sa ‘yan gulmamaki ke yawo daga nan zuwa can, saidai ba wadda ta yi ƙarfi kamar ta alaƙanta cikin da fitacce kuma shahararren mai kuɗin nan kuma mijin jaruma a masana’anatar Regina Deniels, wato Ned Nwoko, wanda ya yi fice a yawan auren mata.

Lamarin wanda ya haifar da maganganu masu ƙarfi da tasiri ga ma’abota kallo da bibiyan jaruman, ya kai ga wata majiya ta tabbatar da fitaccen mai kuɗin ne uban cikin da ke tare da jarumar, kuma ya yi alƙawari tare da shirin auren ta ta zama matar shi ta bakwai.

harwayau dai rahoton ya sake faɗar cewa, matarsa amarya, kuma jarumar fim, Regina Deniels, ta yanke jiki ta faɗi a lokacin da ta ji labarin auren jaruma Chika Ike da mijin nata wanda ta aura a matsayin budurwa da ta kai budurcinta gidansa zai yi.

A daidai lokacin ne mutane suka shiga faɗar albarkacin bakinsu, inda wasu ke ganin wautar jaruma Regina na damuwa da sha’anin mijinta da matan da yake tarawa, kasancewar ta same shi da mata har biyar inda ta zama ta shida.

Wasu kuwa na tausaya mata, kasancewar ta aure shi da ƙarancin shekaru, don haka ba lallai ta san abinda ta sa kanta a ciki ba, sakamakon rashin mallakar hankalinta a lokacin.

Wasu kuwa sun dasa wa lamarin alamar tambaya, sakamakon ɗan kasuwar kuma ɗan siyasa Ned Nwoko, ya sha faɗar kwaɗaituwa ga auren macen da ke kai budurcinta gidan mijinta, wanda yake yawan yabon matarsa jaruma Regina Daniels da hakan, hakan ke nuni da yiwar ba zai iya sake auro matar da yake tunanin ba ta tare da budurcinta.

Da wannan ne ma a ‘yan watannin baya aka zargi alaƙar aure tsakaninsa da jarumar barkwanci kuma ƙaramar yarinya Emmanuala, wanda har ta kai ake faɗar har ya biya kuɗin aurenta, dalilin ta shiga cikin irin tsarin matan da yake son aura, kuma sun ga yana sinsinar takalmi, wanda ake ganin ba dalilin da zai sa kare ya shinshini takalmi idan ba ɗauka zai yi ba.

Wannan dalilin ne ya sa suke ganin abin da kamar wuya, kasancear jaruma Chika cikin jerin matan mai kuɗin, kasancewarta mai shekaru, kuma ɗauke da ciki, baya ga yiwar ko da akwai alaƙa tsakanin ta da ɗan kasuwar, da yiwar ba shi ta fara sani a matsayin ɗa namiji ba.

Shirun da ya yi yawa daga wurin jaruma Chika ne ya ƙara rura wutar zargi a tsakanin masoyansu wanda har ta kai ga wasu ke jafa kalaman ɓatanci da nuna rashin jin daɗin abin ga jarumar da kuma ɗan kasuwa Ned, yayin da wasu ke haɗawa har da jaruma Regina.

A jiya ne, jaruma Chika Ike ta karya azumin da take yi kan lamarin, inda ta wallafa a shafinta na Instagram tana mai ƙaryarawa tare da watsi da raɗe-raɗin da ake yi na alaƙanta cikinta da ɗan kasuwa kuma mijin abokiyar sana’arta Ned Nwoko.

A rubutun jarumar ta ƙara da nuna takaicinta kan yadda ake ta yaɗawa tare da rura wutar jita-jita kan abinda ya dangance rayuwarta, inda ta bayyana hakan a matsayin abinda bai dace ba.

Daga ƙarshe jaruma Chika ta bayyana cewa, tana matuƙar mutunta sirrinta, kuma ita ce za ta zaɓa wa kanta ababen da za ta sanar da mutane dangane da rayuwarta da kuma wanda zata bar wa kanta. Wanda hakan na nufin ba za ta bayyana uban cikin da take ɗauke da shi ba, sai lokacin da ta yi sha’awar hakan, saidai ta tabbatar da ba na ɗan kasuwa Ned ba ne.

Ned Nwoko ya kasance babban ɗan kasuwa, kuma shahararren mai kuɗi, ɗan siyasa da ke da sha’awar mu’amalantar masana’antar Nollywood, musamman matan da ke cikin ta. Wannan ya sa maganganu da dama sun sha fita game da shi, waɗanda suka haɗa da masu kyau da akasin hakan.

Sunan Ned ya ƙara fita ne a lokacin da ya auri Jaruma Regina Denials, a lokacin da take da ƙarancin shekaru, kuma take kan ganiyar shanawa a masana’antar. Wannan ya haifar da karkasuwar ra’ayi, inda wasu ke ganin rashin dacewar haka duba da shekarun ta da kuma na shi. Har ta kai wasu suka dasa ƙiyayyarshi a zuciyarsu, wadda aka samu sauƙinta a hankali, sakamakon irin rayuwar da jarumar ke nuna tana yi a gidan mijin nata ta jin daɗi da kuma farin ciki.

By ukarofi