Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Sakataren Cibiyar Cigaban Musuluncu na al’ummar ƙabilar Eggon na duniya baki ɗaya Malam Umar Galle ya ce bana kimanin ɗalibai ‘yan atsalin jihar Nasarawa dake karatu a jami’o’i daban-daban su 857 ne suka amfana da tallafin karatu da cibiyar ke basu wato Schoolarship a turance a kowace shekara don cigaba da karatunsu.
Malma Umar Galle ya bayyana haka ne a wata zantawa ta musamman da yayi da ‘yan jarida a ofishin cibiyar dake Nasarawa-Eggon hedikwatar ƙaramar hukumar Nasarawa-Eggon a jihar Nasarawa ranar Talata 21 ga watan Oktoban shekarar 2023 da ake ciki.
Ya ce ba shakka tallafin na bana shine mafi yawa da cibiyar ta bai wa ɗaliban dake karatu dake karatu a zangon karatun shekarar 2023 da 2024 don bayan shekaru 10 da kafa ta.
A cewarsa daga cikin ɗalibai 857 da suka amfana da karamcin 526 sabbin ɗalibai ne da suka amfana sannan 331 tsofaffin ne.
Har ila yau a cewarsa a cikin ɗalibai 857 din 9 suna karatun Ph. D ne 26 suna M.Sc, 1 yana karatun lauya 1 PGD 481 B.Sc 36 HND 87 NCE 78 ND 27 ND a fannin kiwon lafiya 111 kuma suna karatun ND da kwalejin kiwon lafiya.
Umar Galle ya ƙara da cewa cibiyar tana raba wa duka ɗaliban tallafin karatun ne ba tare da nuna bambancin addini ko ƙabila ko jinsi da ɓangaren karatun ba.
Ya ce cibiyar tana bada tallafin ne don ta tabbata ilimi shine ginshiƙin rayuwa shi ya sa ta yanke shawarar yin haka don bai wa ɗaliban damar cimma burinsu na rayuwa ta fannin karatun.
Daga nan sai Malam Umar Galle ya kuma yi amfani da damar inda ya mika godiyar sa na musamman ga duka hukumomi da ƙungiyoyi da masu bada gudumawa da sauran su daban-daban dake tallafa wa cibiyar a fannoni daban-daban a yayin aiwatar da karamcin tare da haɗin kan ɗaliban da makarantun su daban-daban inda ya yi fatar tallafin zai cigaba da inganta rayuwarsu ta ɓangaren ilimi don amfanar rayuwarsu dama al’umma baki ɗaya nan gaba.
