Ɗalibi ya kashe abokin karatunsa a Faransa

Spread the love

Daga BELLO A BABAJI

A ranar Alhamis ne wani ɗalibi ɗauke da makami mai cutarwa a wata makarantar kuɗi dake Arewa maso Yammacin Faransa ya kashe ɗan ajinsu da raunata wasu uku gabannin a kama shi.

‘Yan sanda sun ce, masheƙin ya farmaki ƴan uwansa ɗalibai ne da wata wuƙa a makarantar sakandare ta Notre-Dame da Toutes-Aides a birnin Nantes da misalin ƙarfe 12:30 na rana, kana daga bisani wasu malamai suka yi ƙoƙarin daƙile harin nasa.

Tuni dai Ministar ilimin ƙasar, Elisabeth Borne ta ce za ta je Nantes tare da Ministan harkokin cikin gida, Bruno Retailleau domin ɗaukar matakan da suka dace game da aukuwar lamarin.

Ministar ta bayyana hakan ne ta shafinta na X, inda ta ce lamarin ya auku ne yayin cin abincin rana, ta na mai jajenta wa waɗanda abin ya shafa gami da jaddada goyon bayanta ga harkar ilimi a ƙasar.

By Babaji