
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Alhamis ne babbar jam’iyyar adawa – PDP, ta gudanar da taron masu-ruwa-da-tsak a Benin, Babban Birnin Jihar Edo ba tare da tsohon gwamnan jihar, Godwin Obaseki ba.
Obaseki, wanda shi ne shugaban jam’iyyar a lokacin da ya ke gwamna, ya daina bayyana kansa a matsayin ɗan PDP ne tun bayan saukarsa daga kujerar mulkin jihar a Nuwamban 2024.
Blueprint ta ruwaito cewa Obaseki ya daina amsa kiran waya tun daga lokacin.
An gudanar da zaman ne da nufin ƙarfafa wa mambobin jam’iyyar gwiwa ganin yadda ake samu sauye-sauyen sheƙar jam’iyyu a ƴan kwanakin nan.
Sanannu daga cikin waɗanda suka halarci taron sun haɗa da tsohon shugaban ma’aikata a zamanin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, Mike Ogiadome; tsohon gwamnan jihar, Lucky Igbinedion; da tsohon ministan harkokin waje, Tom Ikimi.
Sauran sun haɗa da shugaban jam’iyyar a jihar, Dakta Anthony Aziegbemi; ɗan takarar gwamna a zaɓen 2024, Dakta Asue Ighodalo da abokin tafiyarsa, Barista Osarodion Ogie.
