Ɗan jaridar Kano, Ibrahim Ɗan Uwa Rano ya shaƙi iskar ƴanci bayan hadimin gwamnan Kano ya sa an kama shi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ƴan sanda ta sako ɗan jarida mazaunin Kano, wato Ibrahim Ɗan Uwa Rano bayan alla-wadai daga Cibiyar Fasahar Labarai da Ci-gaba, ƙungiyar Amnesty International da wasu ƙungiyoyin al’umma.

Ɓangarorin sun bayyana kamawa da tsare ɗan jaridar a matsayin abinda aka yi ba bisa doka ba da nufin rufe bakin gidajen jaridu.

An tsare Rano ne bisa zargin sa da laifin ɓatanci a ofishin ƴan sanda na Zone 1 Police Headquarters da ke Kano.

Da fari CITAD da Amnesty International sun nemi a gaggauta sako shi ba tare da sharaɗi ba, lamarin da suka kira da saɓa wa ƴancin gudanar da harkar jarida da dokokin Nijeriya.

By Babaji