2023: Ba za mu zaɓi matsafa ba a Akwai Ibom – Mbang

Daga WAKILIN MU

Tsohon Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa (CAN) Sunday Mbang, ya gargaɗi ‘yan siyasar jihar Akwa Ibom masu neman tsayawa takara a zaɓuɓɓukan 2023 da su nesanta kansu da harkokin ƙungiyar asiri.

Mbang ya yi wannan gargaɗi ne sa’ilin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wajen taron addu’a ta musamman da aka shirya wa ‘yan majalisun tarayya daga jihar don nema musu kariya daga cutar korona a ƙarshen mako a Uyo, babban birnin jihar.

Jagoran addinin ya ce Allah ba zai bari duk wani ɗan siyasa a jihar mai mu’amala da tsafi da makamancin haka ya zama gwamna, ko sanata ko samun wani muƙami da yake kwaɗayi a jihar ba.

Yana mai cewa lamarin da tashin hankali matuƙa ganin yadda harkokin matsafa ke ta ƙaruwa a jihar, tare da jaddada cewa mabiya addinin Kirista ba za su mara wa kowane matsafi baya ba wajen neman wani matsayi ko muƙami.

A cewar Mbang, “Ina amfani da wannan dama wajen yim gargaɗi ga ‘yan siyasar da ke da kwaɗayin neman muƙamai a zaɓe mai zuwa da su kame kansu daga tsafe-tsafe in ba haka ba Allah da nake bauta wa ba zai bari su yi nasara ba.

“Ina kira ga jama’ar Akwa Ibom da cewa duk wani matsafi da ya fito takara al’ummar Kirista ba za mu bari ya zama gwamna, ko sanata, ko samun wani matsayi a jihar ba.

“Mutane masu tsafta muke so su zame mana jagorori a matakai daba-daban amma ba sheɗanu ba, sai dai abin takaicin shi ne ‘ya’yanmu suna harkokin ƙungiyoyin asiri. Don haka muke so mu tsaftace mutanenmu ta yadda idan yaranmu suka ga iyayensu sun daina harkar tsafi, su ma sai su daina.

Da yake magana a madadin takwarorinsa, Sanata Bassey Albert daga Mazaɓar Sanatan Uyo, ya yaba da addu’a ta musamman da aka shirya musu. Kana ya nuna godiyarsu ga Allah da ya bar su da ransu suna ƙoƙarin aiwatar da nauyin da aka ɗora musu na wakilcin al’ummarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *