2023: Ba zan nuna wa kowa wariya a mulki na ba, Tinubu ga CAN

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A cikin makon nan ne, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ta tattaunawa da shugabannin Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) a Abuja, inda ya ce, ba zai ware kowa ba idan aka zaɓe shi a zaɓen 2023.

Manufar tattaunawar dai ba komai ne face CAN ta tabbatar da cewa Tinubu ya fahimci buƙatu da muradan Kiristocin Nijeriya ta hanyar bayyana ƙa’idojin da suke so a gabatar a gwamnatinsa.

An gudanar fara taron ne inda aka tattauna da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha.

Waɗanda Tinubu ya zo da su sun haɗa da shugaban majalisar wakilai ta ƙasa, Femi Gbajabiamila da Sanata Orji Kalu.

Hakazalika, gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi, Hope Uzodinma na jihar Imo, Abdulrahman Abdulrazak na jihar da gwamna Ganduje na Kano duk sun hallara.

A cangare guda, akwai ministan ayyuka na musamman, Sanata George Akume da sauran jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki, Vanguard ta ruwaito.

Idan ba ku manta ba, Bola Tinubu ya gamu da cikas daga Kiristocin Nijeriya tun bayan da ya zavi tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.

Kiristocin Nijeriya, ciki har da wasu shugabannin CAN sun bayyana adawarsu da tikitin Musulmi da Musulmi na jam’iyyar APC a matakin shugaban ƙasa.

Har yanzu dai ba a gama warware matsalar ba, amma ana kyautata zaton zaman Tinubu da CAN a halin yanzu aun warware matsalar da ke tsakaninsu.