Daga BASHIR ISAH
A matsayin tunatarwa ga ‘yan Nijeriya, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta jaddada cewa haramun ne amfani da wayar salula a wajen da aka killace don kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓe.
Shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana hakan a wajen taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya ranar Litinin a Abuja.
A jawabinsa, “Bari in yi amfani da wannan dama in tunatar da ‘yan ƙasa cewar, dokar hana amfani da waya a akwatin zaɓe na nan daram,” in ji Yakubu.
Ya ce sun sauya tsare-tsare na rumfunar zaɓe domin hana harkar sayen ƙuri’a.
Taron ya maida hankali ne wajen tattauna yadda za hana amfani da kuɗi a harkokin zaɓen 2023.
Ya kuma samu mahalarta da suka haɗa da Rundunar ‘Yan Sanda, EFCC, ICPC, IPAC da sauransu.
Da yake jawabi Yakubu ya ce wajibi ne ‘yan ƙasa su guji sayar da ƙuri’arsu.
Haka nan, ya ce ya kamata ‘yan ƙasa su ba da tasu gudunmawa wajen hana amfani da kuɗi a tsarin zaɓen ƙasar ta hanyar kwarmata wa INEC da sauran hukumomi idan hakan ta faru.
Shugaban nan INEC ya kuma ce, ɓangarorin da za su taka rawa wajen yaƙi da amfani da kuɗi a harkar zaɓe sun haɗa da cibiyoyin hada-hadar kuɗade, hukumomin addini, sarakunan gargajiya da dai sauransu.
Daga nan, ya yi kira ga jama’a da su ja hankalin jami’an zaɓe a duk lokacin da suka ga ana aikata abin da ba daidai a wajen zaɓe don ɗaukar mataki.
