2023: INEC ta fitar da sabon jadawalin zaɓe

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bada sanar lokacin da zaɓuɓɓukan 2023 za su kankama.

Shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayar da sanarwar haka a wajen taron manema labarai a birnin tarayya, Abuja.

A cewar Yakubu, yadda al’amarin yake a yanzu shi ne, za a gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Ƙasa ne a ranar Asabar, 25 ga Fabrairun 2023, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun dokoki kuwa za su gudana ran 11 ga Maris, 2023.

Yakubu ya ƙara da cewa, an tsayar da sabbin lokutan zaɓen ne daidai da dokokin zaɓe waɗanda suka buƙaci a bayyana lokutan zaɓe aƙalla kwanaki 260 kafin zaɓe.

Haka nan, ya ce nan ba da daɗewa ba za a wallafa ƙa’idojin zaɓe don amfanin jama’a.