2023: Kano ta zarce ko’ina yawan wakilan jam’iyyu

Spread the love

•Yayin da APC, PDP da NNPP suka tura sama da wakilai 1.5

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, a ranar Litinin ta fitar da adadin wakilan jam’iyyu a rumfunan zaɓe da wajen tattara sakamako kamar yadda jam’iyyu suka miqa wa INEC sunayensu don babban zaɓen 2023.

Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa, jimillar wakilan rumfunan zaɓe na jam’iyya 1,574,301 da kuma wakilai 68,057 ne jam’iyyun siyasar ƙasar suka miƙa wa INEC.

A taƙaice dai, Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta tura wakilai 176,223 rumfunan zaɓe a duk faɗin ƙasar; Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tana da 176,558 a faɗin ƙasar; sannan Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party tana da 176,200 a faɗin ƙasar.

Jihar Kano ce ta fi kowace jiha yawan wakilai wakilai 145,393 daga jam’iyyun siyasa uku na APC, PDP da NNPP; Sai Legas da jimillar mutane 98,646 daga jam’iyyun siyasa uku; da Ribas take da 79,795.

Sauran sun haɗa da Jam’iyyar Labour (134,874 PUAs da 4,859 CAs); Accord (83,007 PUAs da 3,358 CAs); Action Alliance (56,459 PUAs da 1,531 CAs); African Action Congress (38,779 PUAs da 1,723 CAs); African Democratic Congress (96,043 PUAs da 3,626 CAs).

Action Democratic Party (44,516 PUAs da 548 CAs); All Progressives Grand Alliance (25,657 PUAs da 933 CAs); Allied Peoples Movement (80,892 PUAs da 3,932 CAs); Action Peoples Party (64, 798 PUAs da 2,546 CAs); Boot Party (13,544 PUA da 620 CA).

National Rescue Movement (87,014 PUAs da 3,805 CAs); Peoples Redemption Party (87,562 PUAs da 3,452 CAs); Social Democratic Party (98,313 PUAs da 3,310 CAs); Young Progressive Party (76,199 PUAs da 3,151 CAs) da kuma Zenith Labour Party (57,563 PUAs da 1,939 CAs)

Jimillar wakilai 27 za su kasance a Cibiyar tattara bayanai ta ƙasa.

Duk da haka, APGA da ZLP ba su da wakilai masu alaƙa da NCC.

Yayin da A, AA, ADC, APC, APM, APP, LP, NRM, PDP, da YPP ke da wakilan jam’iyya guda biyu kowannen su na da alaƙa da NCC, wasu kuma guda ɗaya.

By Editor