INEC ta fara raba muhimman kayan zabe a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da fara rarraba muhimman kayayyakin zaɓe a faɗin Jihar Yobe.

Da yake sanar da fara raba kayan, Kwamishinan Hukumar Zaɓen a Jihar Yobe (REC), Alhaji Ibrahim Abdullahi, a sa’ilin da yake ganawa da manema labarai a reshen Babban Bankin Nijeriya (CBN) dake Damaturu, da safiyar ranar Alhamis.

Ya ce, “A daidai lokacin da ya rage saura kwana biyu a gudanar da zaɓen, abin da suka dace mu aiwatar a halin yanzu shi ne mu tabbatar mun fara raba waɗannan kayayyakin zaɓen zuwa cibiyoyin da muke da su a Jihar Yobe.

”Wanda daga nan kuma za a ɗauki kayayyakin zuwa gundumomi daban-daban tare da karkasa su zuwa rumfunan zaɓe a faɗin jihar Yobe.

“Kuma da zaran jami’an sun bar nan tare da kayayyakin, kamar yadda kuke gani ga su nan, za su tafi da su tare da cikakken matakan tsaron sojojin Nijeriya, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro zuwa lungu da saƙon jihar nan.

“Mun ɗauki wannan matakin ne don tabbacin kayayyakin sun isa wajajen da aka tsara kai su domin rarrabawa a gundumomi da rumfunan zaɓen,” In ji shi.

Haka nan, Kwamishinan ya buƙaci al’ummar jihar waɗanda suka isa jefa ƙuri’a su fito ƙwansu da ƙwarƙwata su zaɓi waɗanda suke so, a ranar zaɓen.

Ibrahim Abdullahi ya ƙara da cewa, ”Wannan muhimmin kira ne saboda idan mutane ba su fito ba, ba za su samu shugabanin da suke so su jagorance su ba.”