2023: Yadda al’amuran zaɓe suka jawo tashin farashin man fetur zuwa Naira 300 kowacce lita

AMINA YUSUF ALI

Dillalan man fetur, a ranar Talatar da ta gabata sun bayyana cewa, tashoshin man fetur na Nijeriya da dama sun daina lodin man fetur a halin yanzu. Hakan ya faru ne sakamakon fargabar abinda ka- je-ya-zo a yayin tattara sakamakon babban zaɓe a faɗin ƙasar nan.

Hakazalika, rahotannin sun bayyana cewa, hakan ya matuƙar jawo tsadar man fetur, inda ake sayar da man fetur a tsakanin Naira 194 zuwa 200 kowacce lita a gidajen man NNPC kaɗai, sai sauran gidajen man na ‘yan kasuwa kuma ake sayar da su a kan Naira 250 zuwa 300 a kan kowacce lita.

Wannan kuwa ya faru ne duk da dagewar gwamnatin tarayya a kan cewa ta ba wa kowa ikon ƙara kuɗin man fetur ba, kuma ba ta yarda a sayar da shi sama da farashin da ta yanka ba ba tare da tuntuɓar masu ruwa da tsakin da suka kamata ba.

Chief Timipre Sylva, Ministan albarkatun man fetur ya bayyana cewa, Shugaban ƙasa bai yarda da ƙarin farashin man fetur ba daga kowanne kamfani ko wani ɓangare na ƙasar nan ba, domin a cewar sa, yanzu ba lokaci ne na ƙarin farashin man fetur ba.

Kamfanin rarraba man fetur na ƙasa, NNPCL suna sayar da man fetur a kan farashin Naira 194 zuwa Naira 195 kowacce lita amma gidajen man ‘yan kasuwa masu zaman kansu suna sayar da shi sama da haka sosai.

Dillalan man fetur sun bayyana cewa, hakan ya faru ne sanadiyyar wasu tashoshin sun daina lodin man fetur saboda fargabar abinda tattara sakamakon da hukumar INEC take yi zai haifar.

“A halin da ake ciki yanzu, tashoshin ba sa lodi sannan kuma ba sa amsar man fetur ɗin. Idan ka kuma kula za ka ga tashoshi da dama a faɗin ƙasar ba sa aiki. Saboda fargabar da zaɓen ya samar”. Inji Sakataren ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu a Nijeriya (IPMAN) na Abuja da Suleja, Mohammed Shuaibu.

Ya ƙara da cewa, mutane suna jira su ji sanarwar sakamakon zaɓen, saboda tsoron tashin hankula kada ya ritsa da tankunansu. Shi ya sa kuma a cewar sa wasu suka yi amfani da wannan damar don cin karensu ba babbaka, inji shi.

Shu’aibu ya bayyana cewa, wannan ya sa ‘yan kasuwa da dama ba sa yawo da motocinsu daga Legas zuwa sauran wurare a ƙasar nan, kamar yadda aka saba kafin zaɓen. Sannan kuma ba sa zuwa Abuja da sauran wurare har sai an ji sanarwar sakamakon zaven.

Shi kuma shugaban ƙungiyar mamallakan gidajen mai na Nijeriya (PETROAN), Billy Gillis-Harry, ya bayyana cewa, dalilin da ya sa gidajen mai masu zaman kansu suke sayar da fetur sama da farashin da gwamnatin ta yarje da shi shi ne, man fetur ɗin ne ya yi wahalar samuwa matuƙa. Sai mutum ya sha wahala matuƙa kafin ya samu, shi ya sa suke sayar da shi da tsada.