2027: An shiga ruɗani bayan PDP tsagin Turaki ya miƙa sunan Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa ga INEC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsagin jagorancin kwamitin riƙo na ƙasa na jam’iyyar PDP, ƙarƙashin Tanimu Turaki, ya ce ya miƙa sunan tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.

Kakakin tsagin, Ini Ememobong ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, inda ya ce baya ga Goodluck Jonathan, sun kuma miƙa sunayen sauran ‘yan takarar jam’iyyar domin shiga takara a zaɓuka daban-daban ga hukumar.

Ya kuma ce wannan matakin na daga cikin shirye-shiryen tsagin na tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Saidai har yanzu babu wata sanarwa daga INEC da ke tabbatar da karɓar sunayen, sannan ɗaya tsagin jam’iyyar bai fitar da wani martani akan matakin ba.

Wannan al’amari ya nuna cewa har yanzu jam’iyyar ta gaza haɗa kan ‘ya’yanta waje guda duk cewa zaɓen na 2027 na cigaba da ƙaratowa.

By Babaji

Leave a Reply