2027: Atiku ya koma ADC a hukumance

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Maitaimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya shiga jam’iyyar ADC a hukumance, lamarin da ke nuna ƙarfafa jam’iyyar yayin tunkarar babban zaɓen 2027.

Atiku ya sanar da haka ne a jiya Litinin ta kafar X, inda ya wallafa hotonsa riƙe da katin zaman mamban jam’iyyar, wadda ke cigaba da maraba da gaggan ƴan siyasa.

Hakan na zuwa ne watanni da sanar da yin murabus ɗinsa daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP tun a watan Yuli, yana mai bayyana rikici na tsawon lokaci da ya dabaibaye ta a matsayin dalilin ficewarsa.

Haka kuma, wannan ci-gaban ya samu ne bayan da ƴan ɓangaren adawa da dama suak zaɓi jam’iyyar matsayin wadda za ta kara da mai mulki (APC) a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kazalika, bayan ficewarsa daga PDP, Atikun ya kuma bayyana farin cikinsa na zama ɗaya daga cikin ƴaƴanta a baya, yana mai mata fatan alheri acikin ayyukanta na nan gaba.

By Babaji