Jerin gwamnonin Nijeriya da aka tsige tun bayan dawowar mulkin dimukraɗiyya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A Nijeriya, batun tsige gwamna ya kasance ɗaya daga cikin manyan rikice-rikicen siyasa da suka taɓa girgiza jihohi tun bayan dawowar mulkin dimukraɗiyya a shekarar 1999.

Halin da Jihar Ribas ta tsinci kanta a ciki a shekarar 2025 ya sake jawo tsoro da cece-kuce, musamman bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar sakamakon rikicin siyasa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da tsohon ubangidansa, kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Rikicin da ya fara da barazanar tsige gwamna ya rikiɗe zuwa mummunan tashin hankali — har ma aka tayar da bom a majalisar dokokin jihar a ranar 29 ga Oktoba, 2023.

Washegari kuma wasu wakilai masu biyayya ga Wike suka ƙaddamar da shirin tsige Gwamna Fubara. Duk da shiga tsakani da Shugaba Tinubu ya yi a lokacin, rikicin bai lafa ba; maimakon haka, ƙungiyoyin ‘yan bindiga na yankin Neja-Delta suka fara barazanar sake ɗaukar makamai idan aka tsige Fubara, sannan suka kai hari kan wasu rumbunan mai a yankin.

A ranar 18 ga Maris, 2025, gwamnatin Tarayya ta ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas tare da dakatar da Gwamna Fubara, majalisar dokoki da majalisar zartarwa baki ɗaya. An naɗa Rear Admiral Ibas (mai ritaya) a matsayin kwantoma na wucin-gadi. Tinubu ya ce, matakin ya zama dole ne domin kauce wa rikicin da ka iya jefa jihar da ma ƙasa cikin wani sabon yanayi na tarzoma.

Idan Fubara aka tsige ta hanyar majalisa, zai shiga cikin jerin gwamnonin da aka taɓa tsige wa a tarihin Nijeriya – ciki har da Ayodele Fayose, Murtala Nyako, Peter Obi, Diepreye Alamieyeseigha, Joshua Dariye da Rasheed Ladoja.

Mene ne tsigewa?

A ma’anarsa, tsigewa hanya ce ta doka da ke bai wa majalisar dokoki ko wani shari’ar da doka ta kafa damar fara bincike da tuhuma kan babban jami’in gwamnati saboda aikata babban laifi ko mummunan take dokoki.

A Nijeriya, Sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya fayyace yadda za a tsige gwamna — daga fara tuhuma, zuwa martaninsa, kafa kwamitin bincike, da yanke hukunci. Duk wani kauce wa tsarin doka na iya jawo kotu ta rusa tsigewar, kamar yadda ya taɓa faruwa ga Peter Obi, Pan Joshua Dariye, Murtala Nyako da Rasheed Ladoja.

A yau ga jerin gwamnonin da aka tsige tun 1999 zuwa yanzu:

1. Murtala Nyako – Jihar Adamawa:

Majalisar dokokin Adamawa ta tsige Nyako a ranar 15 ga Yuli, 2014, bayan samun sa da laifukan mummunan gudanarwa har guda 16. Duk da haka, daga baya Kotun ɗaukaka ƙara ta soke tsigewar saboda rashin cikakken bin doka. Sai dai an yi latti domin wa’adinsa ya riga ya ƙare.

2. Diepreye Alamieyeseigha – Jihar Bayelsa:

An tsige shi a 9 ga Disamba, 2005 kan zargin rashawa, karkatar da kuɗaɗen gwamnati da kuma laifin almundahanar kuɗaɗe a ƙasashen waje. An gano muhimman kadarori da daloli adadi mai yawa da ake zargin mallakarsa ne ta hanyar almundahana.

3. Ayodele Fayose – Jihar Ekiti:

A 15 ga Oktoba, 2006, majalisar Ekiti ta tsige Fayose da mataimakiyarsa Biodun Olujimi bisa zargin almundahana da karkatar da kuɗin gwamnati. Amma a 2015, Kotun ƙoli ta soke tsigewar, ta tabbatar da cewa an saɓa a Kundin Tsarin Mulki.

4. Joshua Dariye – Jihar Filato:

An tsige Dariye a 13 ga Nuwamba, 2006 bisa zargin cin hanci da haɗama. Amma daga bisani, kotu ta mayar da shi bisa hujjar cewa ba a bi dokokin tsige gwamna yadda ya kamata ba.

5. Peter Obi – Jihar Anambara:

Anambara ta tsige Peter Obi a 2 ga Nuwamba, 2006 bayan watanni bakwai kacal da zama gwamna. Mataimakiyarsa Virginia Etiaba ta zama mace ta farko da ta zama gwamna a tarihin Nijeriya. Amma Kotun ɗaukaka ƙara ta maido da Obi a watan Fabrairu 2007.

6. Rasheed Ladoja – Jihar Oyo:

An tsige Ladoja a 12 ga Janairu, 2006 bayan rikicin siyasa a Oyo. Mataimakinsa Alao-Akala ya gaje shi. Daga baya kotu ta soke tsigewar baki ɗaya, kuma an mayar da shi kan kujerarsa a Disambar 2006.

By ukarofi