
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin ne aka gudanar da janazar waɗannan ƴan sandan da ƴan ta’adda suka halaka a Jihar Bauchi bayn kai musu farmaki a bakin aiki.
An ruwaito cewa, jami’an sun rasa ransu ne a wani ƙauye mai suna Sabon Sara da ke Ƙaramar Hukumar Darazo yayin wani mummunan farmaki da ƴan bindiga suka kai musu a yankin.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Sani Omolori Aliyu ne ya jagoranci taron binne mamatan.
Saidai, babu ƙarin bayani game da yadda aka gudanar da jana’izar a lokacin haɗa wannan rahoton.
A wani labarin kuwa, Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi kira ga Rundunar Sojoji da ta ɗauki wani salo waine magance matsalolin taɓarɓarewar tsaro a ƙasar.
Idris ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Tajudeen Abbas da Gidan Gwamnatin jihar.
Ya kuma nemi a yi bincike game da zargin da ya yi na janyewar jami’an tsaro ƙasa da sa’a guda gabanin awon-gaba da ƴan makarantar Maga 25 a makon da ya gabata.
