Tsakanin Masussuka da Izala kan ’yancin addini da wa’azi

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ

Nijeriya a matsayin kasa mai bin tsarin ‘Secularism’, wato wadda ba ta bin wani addini, a cikin kundin tsarin mulkinta ta tanadar da dokoki kamar haka:

Sashi na 38: Ya yi magana a kan yancin tunani da addini: wanda ya tanadarwa kowanne Dan kasa yancin yin addinin da ya ga dama, ya koma wanda ya so, tare da bayyana imaninsa ga duk addinin da ya yarda da shi ko yayi Imani da shi. Wannan yanci ya hadar da yada addininsa ta hanyar ibada, koyarwa, da aikata shi a bayyane a fili ko a kebance. Sannan da yancin haduwa tare da masu irin akidar domin aiwatar da addininsu.

Sashi na 10: Ya yi maganar tsarin gwamnati wanda baya bin wani addini wanda ya haramtawa ita kanta gwamnatin bin wani kebabben addini, domin tabbatar da adalcin baiwa kowane addini dama bai daya.

Sashe na 45: Na tauye hakki. Ya takaita wadancan sassa domin kada a wuce gona da iri, wato a kare hakkin wasu daga cin zarafin wasu, da kare al’umma, da tsaida doka ko lafiyar al’umma.

Sashi na 40: Ya yi tanadin yancin haduwar mutane na lumana, wanda a cikinsa akwai na haduwa domin aiwatar da ibada ko wa’azi.

Shin a cikin wadannan yanci da kowannen mu ke da shi, akwai wanda Masussuka ya karya? Idan akwai, to abinda ya kamata Izala ta yi shine kai kara kotu a tsarin dokar kasa.

Idan muka juya mahangar musulunci kuma, muna da madogara biyu da zamu duba, wato Qurani da Sunnar Manzo. Da farko dai akwai ayoyi birjik da su ka bada yancin addini kamar:

La ikhra fid Deen

Imma shakiran wa imma kafura

Lakum dinikum wa liyadeen

ƙul kullu ya’amalu ala shakilihi

Fa abudini ma shi’itum min dunih da sauransu.

Wato Allah ya amincewa kowa ya bautawa duk abinda ya ke so babu tsangwama. Kuma a rayuwar Manzo munga yadda ya zauna da kafiran Makka kafin ya yi hijira zuwa Madina, inda ba zama da Yahudu da Nasara ba kawai, har yarjejeniya ta kare juna ya shiga da su. Don haka addinin musulunci ba shi da koyarwar tursasawa. Kuma lokacin da Kiristocin Najran su ka zo Madina domin kalubalantar Annabi da sabuwar koyarwarsa cewa Isa ba Dan Allah ba ne, Annabi ya sauke su a masallacinsa, sun yi muƙabala, ya basu damar yin ibada a cikin masallacinsa mai alfarma (duk da cewa su na ikararin Allah uku da allantar Isa) kuma a karshe a ka watse ba tare da an fahimci juna ba, amma tare da girmama juna.

Sannan a wajen wa’azi sai Allah ya gindaya sharadin cewa; Q16:125 “Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa’azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMafi sani ga wanda ya ɓãce daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.”

Wannan shine kundin tsarin mulkin musulunci, wato duk wanda za ka kira, ka yi amfani da hikima (ba zage zage ba) wajen jawo hankula, kuma a kyautata lafazi (magana Mai kyau), walau wanda ka ke wa wa’azin kafiri ne, ahlul kitabi ko dan’uwa musulmi. Karya wannan kundin tsarin wa’azi na musulunci na daya daga cikin abinda ya kassara mu ya jefa mu halin da muke ciki a yanzu.

Sannan duk idan aka sami rashin fahimta ta wata mas’ala tsakanin musulmi, me Allah ya ce?

Q42:10 “Kuma abin da kuka sãɓã wa jũna a cikinsa kõ mêne ne, to, hukuncinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah.”

Duk inda wani sabani ya bulla, makoma ita ce a koma ga fadar Allah a cikin Qurani. Wannan shine tsarukan da Allah ya gindaya mana. Amma wannan sabuwar hanyar da Malaman Izala ke bi, ta kaucewa koyarwar addini kuma ta dauki salo irin na wasu mutane da Allah ya bamu labari cikin; Q36:18 “Suka ce: “Lalle mũ munã shu’umci da ku! Haƙĩƙa idan ba ku, hanu ba (da yi mana wa’azi) haƙĩƙa, zã mu jẽfe ku, kuma haƙĩƙa wata azãba mai raɗaɗi daga gare mu zã ta shãfe ku.”

Da kuma; Q26:116 “Suka ce: “Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga wa’azin ka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa.”

Wato duk wanda zai razana da wa’azin wani, kuma ya rika yi masa barazana, tabbas ya na daga cikin irin wadannan mutane da ke tsoron gaskiya. Domin matukar dai ka yarda da kanka da gaskiyar da kake adawa, don me za ka hana wani ya fadi nasa ra’ayin, matukar bai keta doka ba? Shin da a ce kowa ya ce gaskiyarsa ita ce kadai gaskiya, shin Izala za ta iya wanzuwa lokacin da ta wanzu?

Abin mamaki sai ga magajin Dr Tanshi, shi kadai na ga ya fito ya na Kiran Malaman Izala da su daina kokarin danne Masussuka da karfin tsiya, domin dada masa farin jini kawai su ke yi. Lokaci ya yi da ya kamata Malaman Izala su farka daga barci su gane cewa zamani ya canza, su rungumi Sunna da gaske ba a baki ba. Su assasa hadin kai da ci gaba da yada kyawawan abubuwa na musulunci a aikace, ba kawai maida hankali a kan hana munanan ba. Domin shi musulunci a aikace, da a tarihance, ya assasa aikata alheri a gaba da hana sharri. Yi, shine farko kafin hani, domin idan yin alheri ya wanzu ya watsu, ba sai ma ka yaki sharrin ba. Alheri shine babban mayakin sharri, kuma alheri ne ya yi karanci a al’ummar musulmi ba kawai a nan Najeriya ba.

Allah ya ganar da mu baki daya kuma ya hade kanmu yadda zamu taru mu yaki masifun da ke karuwa a kullum a wannan yanki na Arewa: masifun talauci, jahilci, ta’adanci, Almajiranci, sake-saken aure, shaye-shaye da sauransu, baya ga barazana daga abokan zaman mu kirista da kuma kasashen yamma. A yanzu muna yiwa makiyanmu aiki ne, ta hanyar yakar junan mu a kullum maimakon yakar matsalolinmu da kuma makiyan mu na ainihi.

By ukarofi