Faɗuwar Sahel: Karyar mayaƙan Rasha – Darussa ga Nijeriya da Afirka

Spread the love

Daga OUMAROU SANOU

•Me ya sa Wagner ta yaudari Afirka — kuma wane darasi Najeriya ya kamata ta hanzarta koya?

•Mayakan haya na Rasha sun yi alkawarin tsaro, amma abin da suka bari shi ne kisan jama’a, wariyar launin fata da mummunar gazawa. Yanzu ‘yan jihadi na bakin ƙofar birane — Najeriya na iya zama gaba.

Birnin Bamako na Mali na sake fuskantar tashin hankali, yayin da Tarayyar Afirka da sauran masu ruwa da tsaki a tsaro ke nuna damuwa kan irin halin da ƙasar ta tsinci kanta. Wannan birnin da ya daɗe yana wakiltar ƙarfin gwiwar Yammacin Afirka, yanzu ya rage a bakin rugujewa — ba saboda mamayar waje ba, sai dai saboda tashe-tashen hankulan ‘yan jihadi da suka daure sun wuce juyin mulki, sun karya kawance, tare da tona asirin alƙawuran “mayar da ikon kasa” da shugabannin soja da abokan aikinsu na Rasha suka yi.

Abin da aka fara tallatawa a matsayin hanyar dawo da zaman lafiya da martaba ya rikide zuwa tashin hankali, jini da cin amana — shaida cewa mayakan haya ba sa kawo zaman lafiya, kuma mulkin soja ba ya iya tabbatar da tsaro mai dorewa. Halin da Mali ta shiga gargaɗi ne ga Najeriya da sauran yankunan Afirka.

ƙaryar da aka sayar wa Mali:

A 2021, bayan shugabannin soja sun kore sojojin Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya, suka kuma rungumi Wagner, mayakan haya na Rasha, sun hure wa jama’a wuta da cewa ‘yan haya za su yi nasarar da dakarun ƙasa suka kasa. Amma bayan shekaru uku, sakamakon ya zama bala’i:

‘Yan jihadi na matsowa bakin Bamako, fararen hula na mutuwa cikin dimbin yawa,
al’ummomi an rushe su, kuma mayakan da aka taɓa yabawa sun bar ƙasar cikin tsananin rikici.

Kididdiga sun nuna cewa fiye da fararen hula 3,000 sun mutu tun zuwan Wagner — kuma da yawa daga hannun mayakan da suka zo “kariya”.

Wariyar launin fata da ra’ayin fifiko:

Shirin da aka fallasa kwanan nan, March on Azawad, ya bankado yadda mayakan Wagner ke wulakanta sojojin Mali da kiran su “marasa ƙarfi” da “makaryata”. Wannan kalami ya yi daidai da irin wariyar launin fata da ke cikin al’adun Rasha, musamman ga yankunan da ba ‘yan asalin Rasha ba kamar Chechnya da Dagestan.

A Moura, Mali, a 2022, rahotanni sun tabbatar da cewa mutane sama da 500 an hallaka su cikin kwanaki biyar. Wani ɓangare na mayakan Wagner ma suna tura hotuna da sakonni cikin wata tashar su ta Telegram mai suna “White Uncles in Africa +18”, suna jin daɗin kisan jama’a da kalaman fifiko.

A gare su, Bafrikawa da ‘yan ta’adda “abu ɗaya ne”.

Manufarsu ba tsaro ba ce — arziki ce:

Mayakan Wagner sun zo Afirka ba don zumunci ba, don zinari suka zo. Gwamnatin Mali na biyan su ba kawai da kuɗi ba — har da ma’adinai, wato sayar da iko don neman tsira. Sun kwace motocin tono ƙasa, motocin sufuri, da babura; sun ɗauki duk abin da suka iya samu.

Halin da ƙasar ke ciki ya tabarbare har ya kai ga mummunar karyewar rundunar tsaro da ƙara ƙarfafa ‘yan jihadi. Rikicin Tinzawaten na 2024, inda mayakan Rasha 84 suka mutu tare da sojojin Mali, hujja ce ta girman kai da rashin dabara.

Duk da cewa an sake masa suna zuwa Africa Corps a 2025, abin bai sauya komai ba. Yau, Bamako na gaban fadowa hannun ‘yan jihadi.

Tasirin wannan ga Nijeriya:

Tashin hankalin Sahel ba ya tsaya a cikin Mali, Burkina da Niger. Kungiyoyin ta’addanci kamar JNIM da ISGS suna matsowa kudu, suna cin gajiyar iyakokin da ba su da tsaro da raunin haɗin kai. A Arewa maso Yammacin Najeriya, an riga an fara ganin:

ƙarin ‘yan gudun hijira, safarar makamai, da yaɗuwar tsattsauran ra’ayi.

Idan Bamako ta fadi, zai buɗe wata sabon hanyar ta’addanci daga arewacin Afirka zuwa Tekun Guinea — barazana ga ƙasashen yankin.

Najeriya na kan hanya, amma tana buƙatar hanzari:

Abin da ke bambanta Najeriya shi ne: ba ta mika ikon tsaronta ga mayakan haya ba. Duk da kalubale, a yanzu tana ci gaba da dogaro da dakarunta, masu ƙarƙashin kundin tsarin mulki, tare da yin aiki da ECOWAS da MNJTF.

Amma akwai manyan matsaloli:

ƙarancin kuɗi, cin hanci, lalacewar tsarin leken asiri, da ƙorafe-ƙorafe kan cin zarafi.

Sabuntawa a bangaren tsaro ba zaɓi ba ne — dole ne.

Najeriya na buƙatar: tsaro mai dogaro da jama’a, zuba jari ga dakarunta, ƙarfafa leken asiri daga al’umma da magance tushen rikici: talauci, rashin adalci da shisshigi na siyasa.

Darasi ga Afirka:

Darasin Sahel ya yi tsawo kuma ya yi muni:

Mayakan haya ba sa ceto ƙasa — suna tsotsar albarkatunta.

Juyin mulki da ake rufa wa baya da sunan “ikon ƙasa” ba ya warware komai — sai ƙara dagulewa.

Zaman lafiya na Afirka dole ya ginu ne kan: gaskiya da amana, haɗin kai na yanki da karɓar gaskiyar mu da matsalolinmu.

Halaka Mali madubi ce. Yana nuna mana abin da ke faruwa idan an maye gurbin dabarar tsaro da ruɗani, kuma an maida “ikon kasa” makamin danniya.

Idan Bamako ta fadi, zai zama gargaɗi ga dukkanmu.

Najeriya dole ta koyi darasi, ta yi aiki cikin gaggawa — ta zama jagora, ba mai jiran abin ya same ta ba.
Oumarou Sanou masanin siyasa da tsaro ne a yankin Sahel. Yana nazarin mulki, rikice-rikice da sauyin siyasa a Afirka. Za a iya tuntuɓar sa a imel ɗinsa [email protected]

By ukarofi