2027: Ba a ga sunan Pantami ba bayan INEC ta fitar da sunayen ‘yan takarar gwamna na ƙarshe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta cire sunan tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami na Jihar Gombe daga jaddawalin ƙarshe na sunayen ‘yan takarar gwamna da za su fafata a watan Fabarairun 2027.

Pantami, wanda da fari sunansa ya fito a jaddawalin da aka wallafa a ranar 29 ga Agusta, an bayyana cewa babu shi acikin na ƙarshen da aka fitar a daren Asabar wayewar Lahadi. A ranar 19 ga Mayu, 2026 ne aka fitar da shi a matsayin ɗan takarar gwamnan Gombe na jam’iyyar PDP bayan ficewarsa daga jam’iyyar APC.

Cire sunan nasa na zuwa ne bayan watanni ana rikicin shari’a kan sahihancin takararsa, ciki har da rikicin zaɓen fidda gwanin PDP da bayanin hukunce-hukuncen Dokar Zaɓe ta 2026. Ahmed Mailantarki, wanda ɗaya ne daga cikin ‘yan takarar PDP, ya ƙalubalanci fitar da Pantami da PDP ta yi da fari a matsayin ɗan takararta na gwamna a jihar a kotu.

Wannan al’amari ya sa Babbar Kotun Gombe ta soke matakin PDPn farkon tare da umartar a sake gudanar da zaɓe. Bayan biyayya ga umarnin kotu da jam’iyyar ta yi, Pantamin ya lashe zaɓen fidda gwanin domin wakiltar PDP a zaɓen 2027 a Gombe.

Saidai, Kotun Ƙoli ta tayar da wasu tambayoyi da suka shafi cancantarsa. Wannan ya zo ne a ranar 24 ga Satumba, a lokacin da kotun ta yi hukuncin dawo da Sashen Dokar Zaɓe na 77(5), (6), (7) da 84(2). Hukunce-hukuncen waɗannan sashe sun haramta wa jam’iyyun siyasa shigar da ‘yan takara da sunayensu ba sa cikin jaddawalin masu rajista da aka miƙa wa INEC a lokacin da aka iyakance, wanda hakan ya haifar da fargabar sahihancin cancantar Pantami shiga zaɓen a dokance.

Daga cikin waɗanda aka zayyano a jaddawalin akwai Bala Bello Tinka na African Democratic Congress (ADC), Jamilu Isyaku Gwamna na APC da Babayo Ardo Kumo na Nigeria Democratic Congress (NDC). Sauran sun haɗa da Zubairu Mu’azu Halilu na Labour Party, Lamela L. Silas na Allied Peoples Movement (APM), Ibrahim Jalo Abubakar na People’s Redemption Party (PRP) da Adamu Mohammed Ma’aji na Social Democratic Party (SDP).

Jaddawalin ƙarshen da INEC ta fitar na wakiltar ‘yan takarar da ta tantance su shiga zaɓen gwamnan duk da cewa tasirin siyasa da shari’a n cire Pantami za su cigaba zama abin ɗaukar hankalin a zaɓen gwamnan na Gombe. A baya dai INEC ta yi ishara da cewa akwai yiwuwar fasarar da Kotun Ƙoli za ta yi wa Dokar Zaɓe ta shafi shigar wasu jam’iyyu da ‘yan takararsu zaɓukan 2027.

By Babaji

Leave a Reply