Daga AISHA ASAS
Wata gobara da ta tashi a Film City da ke Mumbai a ranar Litinin, ta jefa masana’antar fina-finan Indiya cikin damuwa, bayan wutar ta kama wani set ɗin Pati Patni Aur Panga 2 tare da bazuwa zuwa wani wurin da ake shirya Hustle 5.
Rahotanni sun ce gobarar ta tashi da misalin ƙarfe 4 na yamma a wani set da ke Prime Focus Studio, Goregaon, kafin ta bazu zuwa wani set da ke kusa. Duk da girman wutar, babu rahoton mutuwar mutum ko wani rauni, yayin da aka kwashe ma’aikata daga wuraren da ke cikin haɗarin.
Amma lamarin bai tsaya ga kashe gobarar kawai ba. Kungiyar All Indian Cine Workers Association (AICWA) ta rubuta wa gwamnatin Maharashtra tana neman a gudanar da cikakken bincike tare da ɗaukar matakin shari’a kan abin da ta kira yiwuwar sakaci wajen tabbatar da tsaron ma’aikata a wuraren ɗaukar finafinai.
Gobarar ta kuma tilasta dakatar da wasu ayyukan fim da shirye-shiryen talabijin da ake gudanarwa a Film City, ciki har da Kaun Banega Crorepati, lamarin da ya nuna yadda hatsarin da ya faru a wuri guda zai iya shafar ayyukan masana’antar baki ɗaya.
AICWA ta ce abin da ya faru ya sake jaddada buƙatar samar da ingantattun matakan kariya daga gobara a wuraren da ake ɗaukar finafinai, musamman ganin yawan ma’aikata da kayan aiki masu tsada da ake samu a irin waɗannan wurare.
