Daga AISHA ASAS
Fitattun ma’auratan Bollywood, Kiara Advani da Sidharth Malhotra, sun sake faranta ran masoyansu bayan sun sanar da cewa suna jiran haihuwar ɗansu na biyu.
Ma’auratan sun bayyana hakan ne a ranar Laraba, 7 ga Oktoba, ta hanyar wani saƙo da suka wallafa tare a shafukan sada zumunta, inda suka bayyana farin ciki da godiyarsu kan sabon ɗan da suke jira.
Kiara da Sidharth sun yi aure a shekarar 2023, sannan suka samu ɗiyarsu ta farko, Saraayah, a watan Yuli na 2025. Sanarwar haihuwar ta biyu ta jawo saƙonnin taya murna daga abokan aikinsu da sauran fitattun mutane a Bollywood.
