Daga AISHA ASAS
Hollywood ta yi rashin fitacciyar jaruma Eva Marie Saint, wadda ta rasu tana da shekara 102, bayan ta shafe sama da shekaru sittin tana taka rawar gani a finafinai da talabijin.
Saint ta shiga tarihin Hollywood tun daga fim ɗinta na farko, ‘On the Waterfront’, na shekarar 1954, inda ta fito tare da Marlon Brando kuma ta lashe lambar yabo ta Oscar saboda rawar da ta taka. Daga bisani ta ƙara samun shahara bayan ta fito a ‘North by Northwest’ na Alfred Hitchcock tare da Cary Grant.
A tsawon rayuwarta, ta yi aiki tare da wasu manyan daraktocin Hollywood, sannan ta samu Emmy Award bayan aikinta a talabijin. Saint ta rasu a gidanta da ke Los Angeles sakamakon mutuwar da ta riske ta, inda ta bar tarihi mai tsawo a masana’antar finafinai ta Amurka.
