Daga AISHA ASAS
Hollywood ta shiga wani sabon babi bayan Paramount Skydance ta kammala yarjejeniyar sayen Warner Bros Discovery a wata babbar mu’amala da darajarta ta kai kusan dala biliyan 110, inda aka haifi sabon katafaren kamfanin nishaɗi mai suna Skydance.
Haɗewar ta tattaro wasu daga cikin manyan sunayen Hollywood a ƙarƙashin kamfani guda, ciki har da gidajen finafinai da ke bayan Mission: Impossible, Harry Potter da DC Studios, tare da manyan dandamali da kafafen yaɗa labarai kamar Paramount+, HBO Maɗ, CBS da CNN.
David Ellison ne zai jagoranci sabon kamfanin, yayin da aka tsara rage wasu daga cikin kuɗaɗen gudanarwa da kusan dala biliyan shida. Sai dai haɗewar na zuwa da babban nauyin bashi, wanda ya kai kusan dala biliyan 80, lamarin da zai sanya sabon kamfanin fuskantar babban aiki wajen haɗa tsarin kamfanonin biyu da kuma rage kuɗaɗe ba tare da rage ƙarfin samar da finafinai da shirye-shirye ba.
