2027: Ministan Ilimi ya yi alƙawarin kawo wa Tinubu ƙuri’u miliyan 10

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya ce bangaren ilimi na da burin tattara kuri’u miliyan 10 domin sake zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Alausa ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin taron farko na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai kula da Wayar da Kan Bangaren Ilimi, inda ya buƙaci mambobin kwamitin su faɗaɗa ayyukan wayar da kai daga makarantu zuwa al’ummomi daban-daban a faɗin ƙasar.

Ministan ya ce yawan ɗalibai, malamai, malaman jami’o’i, masu gudanar da makarantu, majalisun gudanarwa, ƙungiyoyin ƙwararru da sauran masu ruwa da tsaki a fannin ilimi ya sanya bangaren cikin matsayi na musamman wajen samar da gagarumin rinjaye na kuri’u.

Alausa ya ce idan aka yi aiki tukuru, ana sa ran bangaren ilimi zai iya tattara kuri’u miliyan 10 domin Tinubu a zaɓen 2027.

Ya ce ci gaba da mulki na da muhimmanci domin ba gwamnatin Tinubu damar kammala da kuma ƙarfafa sauye-sauyen da ta fara, musamman a fannonin tattalin arziki, zuba jari da bunƙasa jari-hujjar ɗan Adam.

“Nijeriya na buƙatar ci gaba. Wannan ƙasa, wannan Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sauya al’amuran Nijeriya,” inji shi.

Ya ce ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da gwamnati ta fara na buƙatar lokaci, yana mai cewa wa’adi na biyu ga Tinubu zai ba gwamnati damar ƙara ƙarfafa nasarorin da ta samu tare da samar da ƙarin damarmaki ga ’yan Nijeriya.

Alausa ya buƙaci mambobin kwamitin su tattara mabiyansu da masu ruwa da tsaki a sassan ilimi tare da gina goyon baya mai faɗi ga Tinubu gabanin zaɓen 2027.

Ya ce cimma burin kuri’u miliyan 10 zai buƙaci haɗin kai, aiki tare da kuma ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki a dukkan sassan fannin ilimi.

Kwamitin ya kafa ƙananan kwamitoci da za su kula da jami’o’i, kwalejojin kimiyya da fasaha, kwalejojin ilimi, malamai, majalisun gudanarwa, ilimin fasaha da koyon sana’o’i (TɓET), masu ba da shawara da sauran ƙungiyoyin masu ruwa da tsaki a fannin ilimi.

Ana sa ran waɗanda Shugaban ƙasa ya naɗa a bangaren ilimi za su yi aiki tare da babban kwamitin da ƙananan kwamitocin domin daidaita ayyukan wayar da kai da yaɗa saƙon kamfen zuwa ga masu ruwa da tsaki da al’ummomi a faɗin ƙasar.

Alausa, wanda ke jagorantar kwamitin, ya sake jaddada aniyarsa ta jagorantar wannan yunƙuri da kansa tare da sauran mambobin kwamitin domin cimma burin tattara kuri’u miliyan 10 daga bangaren ilimi.

By ukarofi

Leave a Reply