Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Jam’iyyar ADC na ƙasa, David Mark, ya bayyana rikicin da ke addabar jam’iyyar a matsayin “ƙalubalen da aka saba gani”, yana mai jaddada cewa ba za a iya murƙushe muradun ‘yan adawa ta hanyar matsin lamba na shari’a ko na hukumomi ba.
Mark ya bayyana haka ne a yayin babban taron jam’iyyar na ƙasa na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja, inda ya yi jawabi gaban ɗumbin wakilai da magoya baya a cikin yanayi mai cike da zafin siyasa.
A cikin jawabinsa, tsohon Shugaban Majalisar Dattawan ya ce manufar jam’iyyar ba wai kawai neman mulki ba ce, illa wani nauyi ne na tabbatar da cewa siyasa na iya samar da ingantacciyar rayuwa ga al’umma.
“Ba wai kawai neman nasarar siyasa muke yi ba, muna ganin wannan a matsayin alhakin da ke kanmu da kuma na gaba domin mu tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa dimokuraɗiyya na iya kawo sauyi mai kyau,” inji shi.
Ya bayyana halin da ake ciki a matsayin wani lokaci mai matuƙar muhimmanci, yana kira ga shugabannin adawa daga kowane ɓangare su haɗa kai domin ceto ƙasar daga abin da ya kira barazanar koma-baya ga dimokuraɗiyya.
Mark ya kuma bayyana taron a matsayin ɗaya daga cikin muhimman tarurrukan siyasa a tarihin Nijeriya, yana mai cewa muhimmancinsa ya ta’allaka ne da tsayin daka da jam’iyyun adawa ke yi wajen ci gaba da wanzar da dimokuraɗiyya.
Ya ƙara da cewa amincewarsa da jagorantar jam’iyyar ya samo asali ne daga ƙudurin sake gina Nijeriya tare da mayar da ADC wata babbar kafa ta sauyi.
Sai dai ya koka kan matsalolin da jam’iyyar ta fuskanta, ciki har da zargin cin amana da kuma katsalandan daga wasu hukumomi, musamman dangane da rawar da INEC ke takawa.
A cewarsa, wasu masu ƙarfi da ba su son haɗin kan ADC sun yi amfani da kotuna da kuma hanyoyin gwamnati domin daƙile ayyukan jam’iyyar, har ma da hana gudanar da taron.
Duk da haka, Mark ya jaddada cewa jam’iyyar ba za ta ja da baya ba, yana mai gargaɗin cewa matsin da ake yi na iya jefa Nijeriya cikin tsarin jam’iyya guda ɗaya.
“Ba za mu miƙa wuya ba, domin abin da ke cikin haɗari ba jam’iyya kaɗai ba ce, makomar dimokuraɗiyyar Nijeriya ce gaba ɗaya,” inji shi.
Ya kuma bayyana cewa duk wani yunƙuri na murƙushe jam’iyyar ya ƙara ƙarfafa haɗin kan mambobinta da faɗaɗa goyon baya daga al’umma.
A ƙarshe, ya tabbatar da cewa ADC za ta ci gaba da mayar da hankali kan jin daɗin ‘yan Nijeriya tare da dawo da amincewar jama’a ga makomar ƙasar.
