
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kamfanin sadarwa na Airtel ya sanar da dakatar da bayar da bashin katin kira da data ga kwastomominsa a Nijeriya.
Sanarwar ta fito ne a matsayin wani ɓangare na gyare-gyaren da kamfanin ke yi domin inganta ayyukansa da kuma daidaita su da sabbin ƙa’idoji da ke jagorantar harkokin sadarwa a ƙasar.
A cewar kamfanin, matakin na da nufin tabbatar da ingantaccen tsarin gudanarwa da kuma rage matsalolin da ke tattare da tsarin bashin kira da ake bai wa masu amfani da layinsu.
Sai dai, wannan mataki na iya shafar wasu kwastomomi da suka saba amfani da damar bashin kira musamman a lokutan gaggawa.
Kamfanin ya kuma tabbatar da cewa zai cigaba da samar da wasu hanyoyi na daban domin sauƙaƙa wa kwastomomi amfani da ayyukansa cikin sauƙi da inganci.
Wannan mataki ya jefa miliyoyin ‘yan Nijeriya da suka dogara da ciwo bashin katin waya a lokutan gaggawa fara fuskantar ƙalubale, wanda ya biyo bayan takwaransa na ƙasar Sourth Afrika wato MTN da ya ɗauki irin matakin a ‘yan kwanakin nan.
A wani labarin kuwa, kamfanin sadarwa na MTN a Nijeriya ya dakatar da tsarin bayar da bashin katin kira da data bayan gabatar da sabuwar buƙata da Hukumar kula da Gasa da Bada Kariya ga Kwastomomi (FCCPC) ta yi, wanda ke nuna an samu takura na bayar da rance a fagen dijital a ƙasar.
Rahotanni sun bayyana cewa babban kamfanin sadarwar ya bayyana haka ne a wata takarda da ya miƙa wa Kamfanin Canji na Ƙasa a ranar Alhamis, inda ya ce an dakatar da tsarin ne na wucin-gadi wanda ya zama wajibi sakamakon tabbatar da bin dokokin FCCPC, laturoni, da kuma na tsarin ba wa kwastomomi aro.
Tsarin, wanda ake kira da Xtratime, fage ne da masu amfani da layin da dama suke amfani da shi a Nijeriya domin karɓar rancen kuɗin kira ko data, inda suke biya yayin da suka sayi kati na gaba, wands mafita ne na gajeren zango ga miliyoyin masu amfani.
A saƙon, wanda Sakataren kamfanin, Uto Ukpanah ya fitar, MTN ya bayyana cewa, an soke tsarin a ƙarƙashin sababbin dokokin da aka kafa, waɗanda sun haɗa da tilasta ƙarin buƙatar wasu lasisi da bin hanyoyin da bin dokokin da masu bada bashin dijital suka samar.
Duk da wannan al’amari, MTN ya jaddada wa kwastomominsa cewa sauran shafukan sayen kati ko data sun cigaba da aiki yadda aka tsara, yana mai tabbatar musu da samun sabis mai ƙarfi a gare su.
