Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Duk da yarjejeniyar tsaron bututun mai da aka bai wa kamfanonin Tantita da Maton na biliyoyin naira, rahotanni sun nuna cewa sun kasa rufe dukkanin ruwan Nijeriya yadda ya kamata, lamarin da ya bai wa wasu masu aikata laifi damar gudanar da sata ba tare da an gano su ba.
Sai dai rundunar sojojin ruwa ta Nijeriya ta samu nasarar cafke jiragen ruwa guda biyu, MT Mkpodu da MT Westaf AF, ɗauke da sama da tan 939 na ɗanyen mai da ake zargin an sata, wanda darajarsa ta haura Naira biliyan huɗu. Haka kuma, an kama ma’aikatan jiragen guda 26 a yayin wannan samame.
Shugaban rundunar haɗin gwiwa ta Operation Delta Safe a yankin Kudu maso Kudu, Rear Admiral Olugbenga Oladipo, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Kalaba. Ya ce, wannan nasara na nuna jajircewar sojojin ruwa wajen yaƙi da satar ɗanyen mai da kuma sauran ayyukan ta’addanci da ke illata tattalin arzikin ƙasa.
A cewarsa, an samu wannan nasara ne sakamakon ingantattun bayanan sirri da aka samu da tsakar dare ranar 8 ga Afrilu, inda aka cafke jiragen a wani wurin haƙo mai a yankin haɗin gwiwa na Calabar da Akwa Ibom, suna tsaka da aikin sata. Ya ƙara da cewa, an kama MT Mkpodu ne a yayin da take tsotse ɗanyen mai kai tsaye daga rijiyar mai.
Oladipo ya bayyana cewa haɗin gwiwa tsakanin Ofishin Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), da kuma ofishin Babban Hafsan Tsaron ƙasa (CDS), ne ya taimaka wajen samun wannan nasara. Ya ce, Shugaban Rundunar Sojojin Ruwa da na Sojojin Sama sun samar da kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da aikin, inda aka tura jirgin ruwa mai suna NNS SHERE da jirgin sama mai saukar ungulu domin sa ido daga sama da kuma kama jiragen.
Bayan cafke jiragen, rundunar ta kwashe su zuwa tashar jiragen ruwa ta sojojin ruwa da ke Calabar tare da ma’aikatansu.
Haka kuma, Oladipo ya bayyana cewa an sake cafke wani jirgi mai suna MT Steliosk a ranar 10 ga Afrilu, wanda ke nuna ƙoƙarin haɗin gwiwa tsakanin sassan tsaro wajen daƙile satar mai a ruwan Nijeriya.
A nasa jawabin, Babban Kwamandan Rundunar Sojojin Ruwa na Gabas, Rear Admiral Chidozie Okehie, ya yaba da wannan nasara tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da kamo masu aikata laifuka a yankin, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Rundunar Sojojin Ruwa, ɓice Admiral Idi Abbas.
