Atiku ya zargi INEC da kawo barazanar durƙusar da dimukraɗiyya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi Hukumar Zaɓe ta ƙasa Mai Zaman Kanta (INEC), da cewa ana amfani da ita a matsayin wata hanya ta tauye dimokuraɗiyya a Nijeriya.

Atiku, wanda jigo ne a jam’iyyar ADC, ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a taron ƙasa na jam’iyyar da aka gudanar a Rainbow Eɓent Centre da ke birnin Abuja.

A cikin jawabin nasa, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya soki shugaban INEC, Joash Amupitan, yana mai zarginsa da aikata abubuwan da ya kira “ba bisa ƙa’ida ba” tare da nuna cewa ya kauce daga matsayin tsaka-tsaki da ake buƙata daga hukumar zaɓe.

“Ba zan kammala wannan jawabi ba tare da nuna damuwata kan shugaban INEC da kuma hukumar gaba ɗaya ba. A bayyane yake cewa ana amfani da INEC wajen tauye dimokuraɗiyya a wannan ƙasa,” inji Atiku.

Ya kuma aika da gargaɗi mai ƙarfi ga Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, yana cewa ’yan Nijeriya da suka yi fafutukar kafa dimokuraɗiyya ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare ta daga duk wata barazana.

“Atiku ya ce: ‘Mun yi yaƙi da mulkin soja domin kafa dimokuraɗiyya, kuma za mu sake yin yaƙi domin kare ta idan an yi yunƙurin rushe ta.’”

Bugu da ƙari, ya jaddada cewa shugaban INEC ba zai tsira daga tuhumar da ake masa ba idan aka tabbatar da zarge-zargen, yana mai cewa ɓangaren adawa ba zai lamunci duk wani abin da ya saba doka ba.

Haka kuma, Atiku ya soki salon tafiyar gwamnatin shugaba Tinubu, yana cewa muhimman fannoni kamar tattalin arziki, tsaro da ilimi sun tabarbare a ƙarƙashin mulkin na yanzu. Ya buƙaci ’yan Nijeriya da su tashi tsaye domin neman sahihin sauyi da zai magance matsalolin ƙasar.

Wannan zargi na Atiku na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun saɓani tsakanin INEC da jam’iyyar ADC, musamman bayan da hukumar ta dakatar da amincewa da wani ɓangare na jam’iyyar da ke ƙarƙashin jagorancin Daɓid Mark, bisa wani hukuncin kotu.

A martaninta, jam’iyyar ADC ta ƙara matsa lamba tana kira da a sauke shugaban INEC daga muƙaminsa, tana zarginsa da nuna son kai da kuma rashin adalci ga ɓangaren adawa.

Sai dai INEC ta musanta dukkan waɗannan zarge-zarge, tana mai jaddada cewa tana aiki ne bisa tsarin doka da kuma cikakken tsaka-tsaki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Duk da haka, taron ya samu halartar ɗimbin magoya baya da jiga-jigan jam’iyyar, yayin da ADC ke shirin kafa sabuwar Kwamitin Gudanarwa na ƙasa domin tunkarar zaɓen shekarar 2027.

By ukarofi