2027: Gwamnonin APC 22 sun amince da tsayawar takarar Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Yayin da ake cigaba da shirye-shiryen fara yaƙin neman zaɓen 2027, gwamnonin APC sun sanar da amincewarsu ga Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar da zai tsaya wa jam’iyyar a zaɓen Shugaban Ƙasa.

Sun bayyana hakan ne a yayin taron ƴaƴan jam’iyyar na ƙasa da ya gudana a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja, ranar Alhamis.

Shugaban ķungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya tabbatar da hakan a lokacin da ya gabatar da buķatar, inda Uba Sani na jihar Kaduna ya mara masa baya.

Lamarin da ya nuna ƙarfin haɗin kan da ke tsaka gwamnonin jam’iyyar wajen mara wa muradin Shugaba Tinubu na sake neman zama shugaban Nijeriya a karo na biyu.

Da ya ke jawabi, Uzodimma ya ce suna ƙoƙarin ganin cewa Shugaba Tinubu ya samu nasara a jihohinsu a yayin babban zaɓen duba da yadda suka gamsu da tsarin shugabancinsa da gyare-gyare da ya ke yi a fannoni da dama na al’amuran ƙasar.

Amincewar ta biyo bayan irin matakin ne da sauran jagororin jam’iyyar na shiyya da suka cimma waɗanda suka haɗa da gwamnonin Arewa ta Tsakiya a kwanan nan bisa la’akari da tsarinsa wajen kawo ci-gaba da damawa da kowane ɓangaren na ƙasar a gwmanatinsa.

By Babaji