Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya jaddada cewa yana cikin waɗanda za su haɗa ƙawance domin yaƙar gurɓataccen shugabanci.
Peter Obi, tsohon gwamnan Anambra ya ce haɗakar da yake ciki za ta yaƙi shugabanci na zalunci, yunwa da talaucin da suka addabi ‘yan Nijeriya.
Obi ya yi wannan furucin ne a lokacin da yake amsa tambaya daga jaridar ɓanguard kan raɗe-raɗin da ke yawo cewa ya cimma yarjejeniya da Atiku Abubakar.
Rahoton da ke yawo a kafafen watsa labarai ya nuna cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya yi wa Obi tayin takarar mataimakin shugaban ƙasa a 2027.
Bayan haka kuma, rahoton ya yi ikirarin cewa Atiku ya yi alƙawarin yin zango ɗaya kaɗai idan suka samu nasara a zaɓen 2027 da ke tafe.
Wannan jita-jita dai ta ja hankalin ‘yan Nijeriya, waɗanda suka jima suna dakon ganin wane shiri ’yan adawa suke yi na kawar da APC a zaɓen 2027.
Da yake jawabi a wani taron da aka gudanar a Kubwa, inda ya bada gudummawa don gina makaranta da asibiti da cocin Anglican ta shirya, Obi ya ce yana cikin haɗaka amma ta yaai da yunwa da talauci.
A cewarsa, haɗakatr da yake ta banbanta da wacce ake magana domin manufarsa kawo ƙarshen mulkin zalunci, yayewa jama’a yunwa da talauci.
Peter Obi ya ce, “Za ku iya fassara rahoton yadda kuke so, amma ni ina cikin haɗaka ne domin yaƙi da gurɓataccen shugabanci, yunwa da talauci.”
Peter Obi bai musanta raɗe-raɗin cewa zai yi takara da Atiku ba kai tsaye, haka kuma bai tabbatar da cewa yana cikin tawagar ’yan adawa da ke shirin haɗaka gabanin 2027 ba.
