Abuja: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da dama yayin hari a wani rukunin gadaje

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wasu gungun ƴan bindiga sun kai farmaki a Rukunin Gidaje na Grow Homes Estate dake yankin Chikakore a Kubwa, Abuja, inda suka tsare mazauna na sama da sa’a guda.

Wani mazaunin yankin ya ce, lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 12:00 zuwa 1:30 na daren Litinin.

Ɗaya daga cikin ƴan unguwar ya bayyana cewa ya shaidi lokacin da ƴan bindigar suka yi garkuwa da wani mutum da wata mata.

Saidai, bayan gari ya waye an samu matar a rukunin gidajen bayan sako ta da ƴan bindigar suka yi ba tare da sanin dalilin yin hakan ba.

Bayan samun labarin al’amarin ne, sai ƴan sanda suka kai ɗauki cikin hanzari, inda aka samu ba-takashi na tsawon mintuna 30.

Al’ummar yankin sun koka game da faruwar al’amarin, inda wani ɗan yankin ya yi kira ga gwamnati da ta gyara hanyar da ke kai wa zuwa yankin gami da samar da ofishin ƴan sanda a kusa da su domin samun sauƙin kawo ɗauki a yayin bala’i.

Zuwa lokacin kammala rahoton, ba a san haƙiƙanin adadin waɗanda aka yi garkuwa da su ba.

By Babaji